
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ma’aikatar Noma ta ce, saƙon da ta aika na kira ga ma’aikata da su yi addu’o’i da azumi na kwana uku ba a hukumance ya ke ba.
Lamarin da ta ce, ta yi shawara a kai ne da nufin samun yalwataccen abinci ga al’umma a ƙasa.
A ranar 11 ga watan Yuni, 2025 ta fitar da saƙon ta hannun Daraktan gudanar da harkokin al’umma, Adedayo Modupe, inda ta yi kira ga ma’aikatan ma’aikatar da su taru domin gudanar da addu’o’in neman samun yalwar abinci daga gwamnati don al’ummar ƙasa.
An fitar da sanarwar addu’ar ne daga reshen kula da lamuran ma’aikata domin samar da walwalar abinci acikin ma’aikata.
Ma’aikatar ta bayyana cewa, an shirya taron ne duba da yadda ake samun mace-macen wasu daga cikin ma’aikatan, wanda ya haddasa zargi da kama wasu daga cikin ma’aikata.
