Ziyarar Kaduna: Tinubu ya nemi afuwa bisa jinkirin karrama Kanar Dangiwa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya karrama Kanar Abubakar Dangiwa Umar (mai ritaya), fitaccen mai fafutukar tabbatar da dimokuraɗiyya, kuma ɗaya daga cikin masu goyon bayan gwagwarmayar zaɓen 12 ga watan Yuni, da lambar yabo ta ƙasa ta CFR.

Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin ƙaddamar da wasu motocin bas mai amfani da iskar gas (CNG) guda 100 a Kaduna. Samun lambar CFR wata hujja ce ta jajircewa, ƙishin ƙasa da sadaukarwa.

Kanar Dangiwa Umar, wanda ake yi wa kallon “Sojan Dimokuraɗiyya” saboda tsayuwar da ya yi a lokacin fafutukar tabbatar da dimokuraɗiyya a Nijeriya a shekarun 1990, ba ya cikin jerin sunayen karramawar ƙasa da aka bayar a ranar 12 ga watan Yuni wato Ranar Dimokraɗiyyar Nijeriya.

Ware shi ya jawo cece-kuce daga ɓangarori da dama, ganin irin rawar da ya taka a tarihi wajen kare manufofin dimokuraɗiyya a lokacin mulkin soja.

A cikin jawabinsa, shugaba Tinubu ya amince da hakan, ya kuma ba jama’a haƙuri, inda ya ce: “Ba da gangan aka cire Kanar Dangiwa Umar daga cikin jerin sunayen mutanen da aka karrama a ranar Dimokuraɗiyya ba, abin takaici ne, kuma na ba da haƙuri.

“A yau, na gyara hakan ta hanyar sanar da karramawa ta CFR ga Kanar Dangiwa.”

Kanar Umar, wanda tsohon gwamnan mulkin soja ne a jihar Kaduna, ya kasance ɗaya daga cikin hafsoshin da suka fito ƙarara suka soki zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yunin 1993, wanda ake yi wa kallon mafi ‘yanci da adalci a tarihin Nijeriya. Matsayinsa na jajircewa ya ba shi daraja ta ƙasa da kuma dawwama a tarihin dimokuraɗiyyar Nijeriya.

Shugaba Tinubu ya yaba da jajircewar Kanar Dangiwa wajen tabbatar da adalci da gudanar da mulkin dimokuraɗiyya, inda ya nuna cewa ba za a iya mantawa da irin gudunmawar da ya bayar a cikin labarin tafiyar dimokuraɗiyyar Nijeriya ba.

By ukarofi