Yaɗuwar cutar ‘ulcer’ daga mutum zuwa mutum

Spread the love

Daga CHIROMA AMINU ASID

Makon jiya na yi bayani akan wane abinci mai cutar ‘ulcer’ (gyambon ciki) ya kamata ya ci da wanda bai dace ya ci ba, sai dai wasu suna tambaya ta;

Shin mutum na iya kamuwa da cutar ‘ulcer daga wani?

Amsa ita ce; eh.

Bincike ya tabbatar da aƙalla rabin mutanen duniya na fama da cutar ‘ulcer’, wanda tana wahalar da mutane da dama.

Ita ƙwayar cutar ‘H. Pylory’ dangin ‘bacteria’ ce, waɗanda ke da tsananin wayo da wahala wurin kashewa, sannan idan ba a ɗauki mataki ba, to suna iya zama a jikin mutum har abada.

Tana ƙirƙirar gidaje guda uku ta shiga, wanda idan an sha magani zai kashe gida ɗaya ne kawai, idan aka ƙara zai ci gaba har a kashe ta. Mafi yawanmu idan muka sha magani muka ji ta kwanta, sai mu bar shan magani, sai cutar ta dawo.

Idan ƙwayar cutar ‘H Pylory’ ta shiga jikin mutum da farko, tana ƙirƙirar wani sinadari wanda ke daidai da na jikin mutum. Don haka ba za a yi saurin gane ta ba sai ta yi wa mutum illa.

Yadda ake ɗaukar ta:

-Ta hanyar sumbata (kiss). Idan mutum yana da ita, aka yi sumbata, to za ta iya kama wanda ba shi da ita.

-Amfani da kofi ko cokali ɗaya wurin cin abinci. Idan mai ƙwayar cutar ya sha da kofi ko cokali, kai ma ka ɗauka ka sha, za ka iya kamuwa da cutar.

-Amfani da bayan gida ba a tsaftace jiki ba, sannan aka taɓa wani abu. Shi ma za a iya yaɗa ta.

-Amai. Idan mai cutar ‘ulcer’ ya yi amai, ka taɓa aman ba ka wanke jikinka ba, to za ka iya kamuwa da cutar.

-Yawan shan magungunan Nsaid.

Alamominta:

-Jin ciwon jiki na tsawon lokaci.

-Zafin ciki awa 2-3 bayan an ci abinci.

-Zafin jiki ya zo ya tafi lokuta da dama.

-Tsamiyar dare idan ana jin yunwa.

-Zafin ya tafi idan an sha maganinta, sannan ya dawo.

-Rama.

-Rashin jin yunwa.

-Yawan amai.

-Zawayi.

-Ciwon ciki.

-Kwarnafi ko gyashin gamba.

-Aman jini.

-Kashin jini.

Kariya:

-Rage amfani da maganin zafin jiki da yawa, misali; Ibuprofen, Diclopenac da sauransu.

-Kula da tsaftar jiki da ta muhalli.

-Tsaftace bayan gida.

-Barin sumbata ga kowone irin mutum.

By ukarofi