A ƙoƙarinsa na farfaɗo da harkar noma a Najeriya, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da shirin Renewed Hope Agricultural Mechanisation Programme tare da miƙa taraktoci 2,000 da kayan aikin noma ga manoma a faɗin ƙasar nan.
An gudanar da taron a hedikwatar hukumar sarrafa irinn gona ta ƙasa (National Agricultural Seeds Council), dake Sheda, a kan hanyar Abuja zuwa Lokoja.
Shugaba Tinubu ya bayyana wannan shirin a matsayin wata alamar sauyi da za ta ceto Najeriya daga dogaro da abinci daga ƙasashen waje.
“Mun yi alƙawari, kuma yanzu muna cika shi. Wannan shine matakin farko na sauya fasalin noma a ƙasar nan. Najeriya na da ƙasa mai albarka, mutane masu himma, da dabarun fasaha. Lokaci ya yi da za mu tsare kanmu a fannin abinci.”
Shugaban ƙasa ya bayyana cewa wannan shiri zai sauƙaƙa wa manoma, musamman ƙanana, wajen samun damar amfani da na’urorin zamani da rage wahalar aiki da ƙara yawan amfanin gona. Ya ƙara da cewa za a raba taraktocin da tabbatar da adalci da inganci.
Shugaba Tinubu ya yabawa haɗin gwiwar da gwamnatin ƙasar Belarus ta bayar wajen samar da na’urorin, horar da matasa, da kuma sauya fasahar ƙere-ƙere a Najeriya. Ya bayyana Alex Sigman, wani abokin karatunsa a jami’ar Chicago daga Belarus, a matsayin wanda ya sauƙaƙa cimma wannan yarjejeniya.
Ministan noma da tsaron abinci, Abubakar Kyari, ya bayyana cewa wannan shirin ya ƙunshi taraktoci 2,000, na’urorin haɗa girbin amfanin gona guda 10, taron bita da ƙarin ilimi sau 12, da kayan gyaran na’urorin guda 9,000. Ya ƙara da cewa an tsara shirin don sarrafa fiye da hekta 550,000 na gonaki, samar da metric ton 2,000,000 na abinci, da ƙirƙiro guraben ayyuka fiye da 16,000.
“Ba a taɓa ganin irin wannan shiri na zamani a ɓangaren noma a tarihin Najeriya ba. Wannan shine mafi girma da doka da tsari,” in ji Kyari.
Daga cikin manyan baƙi a wajen taron akwai: Shugaban APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje; gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago; wakilai daga majalisar dokoki da ƙungiyar manoma, da sauran abokan hulɗa na ci gaban noma.
