EFCC ta cafke tsofaffin jami’an NNPCL kan zargin badaƙalar Dala biliyan 7.2

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Hukumar EFCC ta tabbatar da cafke tsohon babban jami’in kuɗi (CFO) na kamfanin mai na ƙasa (NNPCL), Umar Isa, bisa zargin hannu dumu-dumu da ya ke da shi cikin badaƙalar dala biliyan 7.2 da ta shafi gyaran matatun mai na Kaduna, Warri da Fatakwal. Hakanan an kama tsohon manajan daraktan matatar mai ta Warri, Jimoh Olasunkanmi, da wasu ƙarin jami’ai.

Rahotanni sun bayyana cewa Umar Isa, wanda ke kula da sakin kuɗaɗe na gyaran matatun, na cikin waɗanda ake zargi da cin hanci da rashawa, karkatar da kuɗaɗe, da karɓar kuɗin hannu daga kamfanonin kwangila. Sauran waɗanda ke tsare sun haɗa da Tunde Bakare, manajan daraktan Warri Refinery; Ahmed Dikko da Ibrahim Onoja, waɗanda suka taɓa jagorantar matatar mai ta Fatakwal.

Wani babban jami’in hukumar ya tabbatar da cewa bincike na gudana a kan dukkanin jami’an da suka taka rawa a harkar gyaran matatun, musamman daga shekarar 2017 zuwa 2023. A cewar majalisar dattawa, akwai bambance-bambance masu yawa a cikin bayanan kuɗi na NNPCL da suka bayyana abubuwan da suka girgiza su.

Kwamitin kula da asusun jama’a na majalisar dattawa, ƙarƙashin jagorancin Sanata Aliyu Wadada, ya miƙa jerin tambayoyi 11 ga hukumar NNPCL tare da bashi mako guda domin bayar da amsoshi.

Wannan ci gaba yana ƙara tabbatar da buƙatar sake duba yadda dukiyar ƙasa ke tafiya a hannun manyan jami’an gwamnati.

By ukarofi