
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu ya yi watsi da ƙudirin dokar yin kwaskwarima ga dokar Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta 2025.
Ƙudirin dokar, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ya ruwaito, na neman a bai wa hukumar ikon mallake wani yanki daga cikin kuɗaɗen da ta tatso a yayin kama waɗanda aka samu da aikata manyan laifukan da suka shafin ƙwaya.
A ranar Alhamis ne a yayin gudanar da zaman Majalisar Wakilai, Kakakinta Tajudeen Abbas ya karanta ƙudirin.
Saidai, a lokacin da ya ke tsokaci game da batun, Shugaba Tinubu, wanda ya kafa hujja da sashe na 58 layi na 4 na dokar ƙasa kundin 1999, ya ce matuƙar aka sanya wa ƙudirin hannu, zai zama yana cin karo da wasu layuka da suka gabace shi.
Tinubu ya bayyana cewa, a dokar da ake aiki da ita a yanzu, akwai batun cewa dukkan kuɗaɗen da aka tara daga manyan laifuka, ana sanya su ne a asusun kuɗaɗen kadarorin da aka ƙwato.
Ya ƙara da cewa, dukkan wasu kuɗaɗe na ababen da aka ƙwato daga masu aikata manyan laifuka da za a bai wa wata hukuma, wajibi ne ya zama daga shugaban ƙasa bayan samun sahalewar Majalisar Zartarwa (FEC) da kuma Majalisar Dokoki.
