Yadda ma’aikacin biredi ya auna arziki bayan ƙarfe ya tsire shi a Argungu 

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Wani mutum mai suna Babangida, wanda ya ke aiki da kamfanin gidan biredin Kampala da ya ke garin Argungu ta Jihar Kebbi ya auna arziki bayan da wani dogon ƙarfe ya ɓalle daga injin gasa biredi ya fito ya tsire shi.

Da ya ke zantawa da Wakilin Manhaja,  Alhaji Mamuda, wanda shine babban manajan gidajen biredin na Kampala, ya ce, shi dai wannan mutumin ƙauyen Gidan Agoda ne da ke ƙaramar hukumar Augie, amma dai yana dillancin biredi ne yana rarraba wa masu shaguna da kuma masu shayi zuwa masu sana’ar sayar da biredi a tashoshin mota da sauran wurare.

Wannan abin ya faru ne ranar Litinin ɗin da ta gabata, yana zaune yana saka biredi ne a cikin leda kafin ya ɗauka daga nan sai wani ƙarfe ya ɓalle daga injimin gasa biredi ya sanadiyyar zafi ya zo ya same shi ya tsire shi.

Daga nan sai aka ɗauke shi da ƙarfen a jiki zuwa babbar asibitin Argungu, inda su kuma suka ɗauke shi zuwa asibitin koyarwa ta Usman Dan Fodiyo da ke Sokoto, inda a can ne aka yi masa aiki kuma yanzu haka yana nan yana samun sauƙi.

Alhaji Mamuda ya ƙara da cewa, wannan dai shi ne karo na farko da ya taɓa samun irin wannan tashin hankali a masana’antarsu, saboda su kan ɗauki matakan kariya, musamman ga waɗanda ke sarrafa injinan gidajen biredinsu.

By ukarofi