APC ta naɗa Bukar Dalori a matsayin shugaban riƙon ƙwarya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mataimakin Shugaban APC na Ƙasa a Arewa, Alhaji Bukar Dalori ya zama sabon Shugaban jam’iyyar na riƙon ƙwarya biyo bayan yin murabus da Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi a ranar Juma’a.

Sashe na 14(2) na kumdin dokokin APC ya bai wa mataimakin shugaban jam’iyyar na Ƙasa damar taimaka wa shugaban jam’iyyar wajen gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyansa.

Zuwa lokacin fitar rahoton, ba a samu cikakken bayanin da ya sa Ganduje yin murabus ba, lamarin da ya jefa ma’aikatan ofishin da masu ziyara cikin ruɗani.

An ruwaito cewa, tsohon gwamnan na Kano ya yi murabus ne bisa wasu matsaloli na cikin gida waɗanda daga ciki akwai batun ɗaukar mataimakin shugaban ƙasa.

Wasu daga cikin sunayen da ake ganin sune waɗanda za a bai wa muƙamin, daga arewa maso yammacin Nijeriya suke, lamarin da ya sa kai-tsaye za a ɗauki shugaban jam’iyya daga wata shiyya.

Wata majiya ta ce, tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Umar Tanko Almakura na ɗaya daga cikin ƴan gaba-gaba da ka iya maye gurbin Ganduje.

By Babaji