Har yanzu Akume ne Sakataren Gwamnatin Tarayya – Fadar Shugaban Ƙasa

Spread the love

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa babu wani canji da aka yi game da matsayin Sanata George Akume a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF).

A cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin bayani da dabarun yaɗa labarai, ya fitar a yau Asabar, an bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu wanda a halin yanzu yake Saint Lucia bai yi wani sabon naɗin muƙami ba.

Sanarwar ta musanta jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta da labarai cewa an sauke Sanata Akume daga muƙaminsa, tana mai cewa wannan labari ƙarya ne da aka ƙirƙira don cimma wata manufa.

Fadar Shugaban Ƙasar ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da irin waɗannan jita-jita da basu da tushe da makama.

By ukarofi