
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMET) ta yi hasashen samun tsawa da yanayi na ruwan sama daga ranar Litinin zuwa Laraba a faɗin ƙasar.
A saƙon hasashen yanayin da ta fitar a ranar Lahadi a Abuja, NiMET ta ce akwai yiwuwar samun hadari ma ɗauke da tsawa a sa’o’in safiya a Jihohin Sakkwato Kebbi, Zamfara, Taraba, Adamawa da Kaduna a Arewacin Nijeriya, a yayin da kuma za a yi rana a sauran sassan shiyyar.
Ta kuma ce, ana tsammanin samun ruwan sama da tsawa a lokutan rana da dare a yankunan Jihohin Adamawa, Taraba, Borno, Jigawa, Yobe, Kano, Katsina, Gombe, Sakkwato, Kebbi, Zamfara da Kaduna.
A Arewa ta Tsakiya kuwa, ana tsammanin ruwan sama da tsawa a safiya a sassan Jihohin Neja, Filato, da Abuja yayin da za a yi rana da hadari a sauran sassan shiyyar, inda a lokutan rana da dare kuma ake sa ran hadari da yiwuwar ruwan sama a Abuja, Nasarawa, Kogi da Neja.
Haka kuma a kudancin ƙasa, ana sa ran samun yanayi na hadari da yayyafi a safiya da maraice a ranakun Litinin da Talata.
A ranar Laraba kuwa, NiMET ta yi hasashen mamakon ruwan sama ɗauke da tsawa a jihohin Arewa, yayin ake tsammanin yayyafi a kudanci.
Hukumar ta shawarci al’umma da su guji tuƙi a cikin mamakon ruwan sama, tare da kashe layukan lantarki domin kauce wa shiga haɗari.
