Bayani kan sha’awa

Spread the love

Tare da SALISU YAKUBU

A jikin kowacce mace da ka sani a duniya, akwai wasu ‘very sensitive areas’ da idan dai ka taɓa su, dole ne sai sha’awar ta ta miƙe, musamman ‘Clitoris, Nipples, Navel’ da kuma tafin ƙafa. A waɗannan wuraren ne ake samun manyan sinadaran tada sha’awa musamman ‘Androgen, Dopamine da Serotonin’. Zaman su a wannan wurin ne yasa koda yaushe maɗaukan sha’awa zuwa ‘sexual mental faculty’ a ƙwaƙwalwa suke kaiwa da komowa dare da rana. Waɗannan maɗaukan sune a kimiyyance muke ƙira da suna “Sensorimotor receptors”. Wannan ‘natural physiology ne irrespective of Africans, Arabs, Asians, Americans ko Latins’. Taɓa waɗannan wuraren ne kamar ‘Kickstarter’ ɗin mace. Ma’ana: dole sai an fara taɓa waɗannan wuraren ne sannan ‘hormones’ ɗin suke fara aiki.
A ɓangaren namiji kuma, yana samun sha’awa mai ƙarfi sannan ya zubar da maniyyin sa ne a duk lokacin da ‘level’ na wani ‘Hormone’ mai suna ‘Testosterone’ ya kai wani mizani. Ma’ana, taɓa wani wuri a jikin namiji kaɗai baya tada masa sha’awa har sai ‘peak level’ na ‘Testosterone’ ɗin nan ya je gejin da ake buƙata – saɓanin mace. Zuwa gejin ‘Testosterone’ ɗin nan ne kamar ‘Kickstarter’ na motsawar sha’awar namiji. Shi wannan ‘Testosterone’ ɗin, ‘ya’yan marainan ka ne suke samar da 80% ɗin shi. Sauran 20% ɗin ana samar da su ne daga jikin ‘Adrenal gland’ dake saman ƙodar ka. Wannan dalilin ne yasa kana fara jin sha’awa, ƙirjin ka yake bugawa da sauri sannan azzakarin ka yake miƙewa da gaggawa saboda a setin ƙirji da ƙugun ka ne shi wannan ‘Testosterone’ ɗin yake fitowa.
’Ya’yan marainan ka da Adrenal glands ɗin nan, suna aiki ne dare da rana. Sannan ba abinda ya shafe su da ra’ayin ka wajen samar da wannan ‘Testosterone’ ɗin saboda tun a tsarin halittar ka, Allah ya ajiye kula da aiwatar da aikin su ne a ƙarƙashin ‘Autonomic Nervous System’. Saidai, idan adadin wannan ‘Testosterone’ ɗin ya kai wani mizani, akwai wasu sashe guda biyu a ƙwaƙwalwar ka wanda sune suke bada damar fito da wannan ‘Testosterone’ ɗin daga ‘ya’yan marainan nan naka da kuma Adrenal gland ɗin – sannan su tantance adadin sa idan yayi yawa ko yayi kaɗan saboda kar ya haifar maka da matsala. Waɗannan sashen guda biyu sune a kimiyyance muke ƙira da ‘Hypothalamus’ da kuma ‘Pituitary Glands’.
Wannan ne dalilin da yasa idan wannan ‘Testosterone’ ɗin ya kai ‘peak level’ a jikin ka, koda bacci kake ya zama dole sai ka zubar da maniyyi wanda muke ƙira da ‘Nocturnal Emission’ a kimiyyance. Idan kuma ka dawo kan mutanen da suke ‘masturbation’ ko masu aure, yana matuƙar wahala ka ga suna zubar da maniyyi lokacin da suke bacci saboda shi wannan ‘Testosterone’ ɗin baya zuwa ‘peak level’ ɗin ma ballantana ya ƙetara iyakar fitowar. Wannan yana daga cikin manyan dalilan da suka sa duk mutumin da ya fiya fitar da maniyyi akai-akai, yana da matuƙar wahala ka ganshi da tsoka mai yawa a jikin sa koda kuwa mutum yana cin abinci mai gina jiki sakamakon 85% na maniyyin namiji ‘protein’ ne. Sannan duk inzali ɗaya na adadin 5ml na sperm, yana ɗauke ne da over 252 milligram na protein.
Bugu da ƙarin wannan bayanin, ba yadda za’a yi kana fitar da maniyyin da ya kai 10ml a rana ka rabu da ciwon kai, kasala da tsotsewar tsoka a jikin ka. Kasan menene dalili? Amsa: Waɗannan halittun na ‘Hypothalamus, Pituitary Glands’, ‘Testicles’ da kuma ‘Adrenal Glands’ ɗin nan ne kake gajiyarwa da ‘eɗcessive workload beyond normal’. Wannan yana daga cikin manyan dalilan da suka sa duk mutumin da yake yawan jima’i, ‘ya’yan marainan sa ƙanana ne fiye da wanda ba ya yi sosai. 
Idan kuma ka dawo ɓangaren mace, yawan jima’i baya haifar musu da matsala a zahiri kamar namiji. Daman su recipients ne ba donors bane. Ma’ana: masu karɓa ne ba masu bayarwa ba. Saboda sperm ɗinka dake ɗauke da 85% na proteins, yana shiga jikin mace ya zama supplements. Wannan yana daga cikin manyan dalilan da suka sa mace take ƙara zama babba sosai sannan fatar jikin ta zama very smooth idan ka kwatanta ta dana namiji musamman idan tana samun abinci da nutsuwa a lokacin tarayyar aure. Haka zalika, hormones ɗin da suke aiki a jikin mace ‘are less busy during seɗual orgasms’ fiye da na namiji. ‘Androgen, Estrogen, Dopamine’ da ‘Serotonin’ sune manyan ‘hormones’ ɗin da suke motsawa mace sha’awa bayan ka taɓa sensitive wuraren nan. 
A jikin namiji kuwa, bayan ita kanta sha’awar ƙwaƙwalwar da kuma aikin ‘Testosterone’ ɗin, akwai ‘Gonadotropin-releasing hormone, Oxytocin, Dopamine, Serotonin, Vasopressin’ da kuma ‘catecholamines’ waɗanda dukkan su ‘Hormones’ ne masu zaman kansu wajen zafafa ƙarfin sha’awa fiye da mace. Wannan ne yasa sha’awar dake tattare da namiji take a bayyane wanda yake sawa mutum ya fitar da ruwan mazi tun kafin ya taɓa jikin mace. Ita kuma mace, sai a lokacin da aka tava waɗannan ‘sensitive area’ ɗin ne ko kuma lokacin da ake tarayyar auren da ita ne take fara jikewa da kuma samun ƙarfin sha’awar. Wannan ne yasa 90% na mata basa yin mafarkin jima’i koda suna cikin tsananin shekarun balaga saboda sai an taɓa su ne sha’awar su take miƙewa.

Salisu Yakubu, RN, RNT, CT
08033990930

By ukarofi