
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Litinin ne Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya jaddada aniyar gwamnati ta haramta gwajin makamin nukiliya a Nijeriya ta haɗin-gwiwa da Ƙungiyar Yarjejeniyar Hana Gwada Nukiliya (CTBTO).
Shettima ya faɗi haka ne a lokacin da ya karɓi baƙoncin Sakataren ƙungiyar, Dakta Robert Floyd a Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja.
Ya ce, babban abinda ke gaban Afirka a yanzu shine ta magance matsalolin talauci da tasirin sauyin yanayi da ke addabar al’umma ba gwada ƙarfin makamin nukiliya ba.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma yaba wa CTBTO bisa ƙoƙarinta wajen tabbatar da kiyaye ƙa’idodin yarjejeniyar yadda ya dace.
Haka kuma, ya jinjina mata wajen kula da kuma taimakawa wajen gano bala’ai da ka iya aukuwa a yankunan ƙasashen da ke ƙarƙashinta da ɗaukar matakan kariya a kansu, lamarin da ya ke taimaka wa tabbatuwar yanayin ƙasashen cikin aminci.
Da ya ke jawabi, Robert Floyd ya yaba wa shugabancin Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu bisa gudunmuwarsa wajen ƙoƙarin samar da hanyoyin rage gwajin makaman nukiliya da sanya takunkumi mai karfi a kai.
Ya bayyana alaƙar Nijeriya da ƙungiyar a matsayin ginshiƙin da ke ƙarfafa wa ayyukan ƙungiyar a matakai daban-daban wajen tabbatar da ta samu nasara a harkokinta.
