
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Malaman Jami’o’in Nijeriya (ASUU) ta shiga yajin aikin gama-gari bisa rashin biyan mambobinta albashin watan Yuni, 2025.
Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ya tabbatar da hakan a Abuja, ranar Litinin.
Ya ce, sun ɗauki matakin ne domin nuna rashin jin daɗinsu ga Gwamnatin Tarayya kan jinkiri da aka samu wajen biyan albashin, inda ya ce ba za su amince da hakan ba.
Farfesan ya bayyana cewa, sakamakon samun jinkirin biyan albashi da suke fuskanta ya sa suka sauya madogara daga tsarin biya ta IPPS zuwa na ‘Government Integrated Financial Management Information System’ (GIFMIS), lamarin da a cewarsa, bai sa ta canza zani ba.
Ya kuma ce, jinkiri ba daga tsarin biyan ba ne, saidai ana samu haka ne daga ofishin Akanta-Janar, wanda da gan-gan ake yin hakan.
Kazalika, Piwuna ya caccaki gwamnati wajen gaza sauke nauyinta musamman na rashin biyan ragowar Naira biliyan 10 da aka amince daga biliyan N50 na alawus ɗin karatu bayan sako N40bn.
