Majalisar Wakilai za ta ƙara kujeru zuwa 552 da bada 83 ga mata

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar Wakilai tana nema yi wa kundin dokar ƙasa kwaskwarima domin bada kaso 10 na kujerun Majalisar Dokoki ga mata da kashi biyar ga nakasassu.

A ƙarƙashin takardar neman gyaran, za a ƙara kujeru 83 a majalisa, inda za a bai wa mata guda 55 a Majalisar Wakilai, lamarin da zai kai adadin ƴaƴan majalisar dokokin daga 360 zuwa 415.

Sai kuma ƙarin kujeru 28 a Majalisar Dattawa, wanda haka zai sa adadin mambobin ya koma daga 469 zuwa 552.

Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas ya sanar da hakan a ranar Talata a Abuja, yayin taron bada ba’asi kan tsakiyar zango na majalisa ta 10, inda ya ce sun bijiro da buƙatar ne da nufin damawa da mata da nakasassu a harkokin majalisar.

Ya ce, kujerun da za a ƙaran, za a cike su ne a yayin da aka yi zaɓuka kai-tsaye ta ƙuri’u daban-daban, sannan jihohi ne za su raba a tsakaninsu don tabbatar da daidaito ga shiyyoyi.

Kazalika, ya bayyana cewa, za a ware kaso biyar ga nakasassun mutane, waɗanda za a bai wa ƙungiyoyi masu fafutukar ƴancin nakasassu da aka tantance damar fitar da ƴan takara.

Haka kuma, za a ba su damar ƴanci da ɗaukar nauyi daidai da na sauran ƴan majalisa.

By Babaji