Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
An yanke wa wata yarinya ‘yar shekara 16 mai suna Joy Afekafe hukuncin ɗaurin rai-da-rai a gidan yari bayan ta kashe wata malamar Jami’ar Fasaha ta Tarayya (FUT) da ke Minna a Jihar Neja.
A shekarar 2023, rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta cafke Joy bayan bincike ya nuna cewa ta kai harin ne tare da abokan karatunta Waleɗ da Smart, waɗanda har yanzu ba a kama su ba.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Wasiu Abiodun, ya ce, “’yan sandan da ke aiki a sashin Bosso sun ziyarci wurin da lamarin ya faru, inda aka samu wuƙaƙe guda biyu ɗauke da jini da ake zargin da su aka yi amfani wajen daɓa mata, inda aka kai gawar zuwa asibitin IBB dake Minna, inda aka tabbatar da mutuwarta.
Abiodun ya ƙara da cewa, “Lokacin da ake yi mata tambayoyi, wadda ake zargin ta amsa cewa ta yi aiki a matsayin ‘yar aikin gidan marigayiyar na tsawon makonni uku, kuma an sallame ta ne saboda mugun halin da ta yi a gidan.
“Bayan an sallame ta, ta haɗu da abokan karatunta, waɗanda ake kira Waleɗ da Smart, ta ba su labarin irin wahalar da ta sha, kuma ta haɗa baki wajen kai wa malamar hari a gidanta.”
Da yake yanke hukuncin a ranar Laraba, Mai shari’a Mohammed Adishetu Mohammed na babbar kotun Minna mai lamba 4 ya ce: “Gaba ɗaya da kuma dukkan dalilan da aka bayyana a cikin wannan hukunci, na yarda da cewa masu gabatar da ƙara sun iya tabbatar da babu shakka cewa Dakta Misis Funmilayo Sherifat Adefolalu ta rasu.
“Cewar mutuwar Drs Funmilayo Sherifat Adefolalu wanda aka yankewa hukuncin ne tare da abokanta, a halin yanzu, lokacin da suka yi amfani da wuƙaƙe suka daɓa mata wuƙa da dama, daga ƙarshe suka buge ta da katako da nufin su kashe ta.
“Daga shaidun da ke gabana, na gamsu da cewa masu gabatar da ƙara sun tabbatar da laifukan kisan kai da ke da hukuncin kisa ga wanda aka yanke masa hukunci.”
Mai shari’a Mohammed ya bayyana cewa, “Ko da yake yanzu tana da shekara 16 a duniya, bisa tanadin sashe na 221 na kundin laifuffuka, dokokin jihar Neja na shekarar 1989, duk wanda aka samu da laifin kisan kai mai hukuncin kisa za a yanke masa hukuncin kisa ta hanyar da alkali mai shari’a ya tsara.”
Sai dai idan wanda aka yanke wa laifin bai wuce shekara 18 ba a lokacin da aka aikata laifin, ba za a bayyana ko rubuta hukuncin kisa ba. A maimakon haka, kotu za ta yanke wa mutumin hukuncin ɗaurin rai da rai ko kuma wasu sharuɗɗan.”
Yanzu haka Miss Joy Afekafe za ta yi rayuwa a cibiyar da ake tsare da ita bisa laifin kisan kai da kuma shekara goma saboda fashi da makami.
