Gyaran matatun Nijeriya kamar sabunta mota ƴar shekara 40 ne, inji Ɗangote

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hamshaƙin Attajirin Ɗan kasuwa, Alhaji Aliko Ɗangote ya koka game da makomar matatun gwamnatin Nijeriya, inda ya ce duk da Dala biliyan 18 da aka kashe wajen gyara su, ba lallai su koma aiki kamar yadda su ke a baya ba.

Ɗangote a yayin ganawa da wata tawaga daga shirin ‘Global CEO Africa Programme’ na
Makarantar Kasuwanci dake Legas, ya ce zai yi wahala matatun Fatakwal, Warri da Kaduna da ke ƙarƙashin kamfanin NNPCL su sake koma wa aiki yadda dace.

Ya ce, an ɗauki shekaru ana ɓarnatar da kuɗaɗe domin dawo da martabarsu duk cewa gwamnatoci da dama sun ta yin alƙawarin gyara su.

A yayin zagaye matatarsa mai fitar da ganga 650,000 a kullum dake Lekki, wanda ake ganin mafita fame da matsalolin shigo da fetur daga waje, Ɗangote ya bayyana bambanci aiki da ke tsakanin tasa da na gwamnati.

Ya kuma hakaito yadda kamfaninsa ya saye matatun a shekarar 2007 lokacin da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ke shirin barin mulki.

Watanni kaɗan bayan haka ne a lokacin marigayi tsohon shugaban ƙasa Umar Musa Yar’Adua aka rushe cikin, bayan wasu jami’an NNPC sun faɗa wa Yar’Adua cewa an sayer da su ne a farashi mai rahusa.

By Babaji