A Santiago Bernabeu za a yi wasan ƙarshe na Kofin Duniya na 2030 – Rahoto

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta cimma yarjejeniya da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) bisa zama mai masauƙin baƙi wajen jagorantar wasan ƙarshe na gasar Kofin Duniya na 2030.

Marca ta ruwaito cewa an cimma yarjejeniyar tsakanin ɓangarori biyun ne a yayin ganawa da Shugaban ƙungiyar Florentino Perez da Shugaban FIFA Gianni Infantino a Amurka, inda ake gudanar da Kofin Duniya na ƙungiyoyi.

Za a gudanar da wasannin Kofin Duniyar ne a ƙasashen Sifaniya, Portugal da Moroko, lamarin da ya zama na farko a tarihi da ƙasashe uku za su jagoranci gasar.

Tun da jimawa, Real Madrid ta ke kamun ƙafa wajen ganin ta zama wadda za ta jagoranci wasan ƙarshe na gasar, wadda filin wasanta na ɗaya cikin filayen wasan da suka fi yin fice ta fuskar ci-gaba.

By Babaji