
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban Rundunar Sojojin sama (NAF), Air Marshal Hassan Abubakar, ya ce rundunar a ƙarƙashin jagorancinsa ta tsayu wajen ganin ta tabbatar da samar da walwala da jin-daɗin jami’an da suka yi ritaya.
Kyaftin Mustapha Suleiman na rukuni, wanda ya wakilci shugaban rundunar ya faɗi haka a sansanin sojojin dake Kano, yayin taron tsofaffin sojojin rundunar da waɗanda suka yi ritaya.
An gabatar da lakcoci, tattauna muhimman al’amuran da suka shafi kula da lafiyarsu da wasu bututuwa.
Da ya ke jawabi a taron, Kyaftin Sulaiman ya bayyana cewa an samar da cibiya ta musamman domin kula da harkokin tsofaffin jami’an don magance musu matsaloli da dama.
Ya kuma ce, rundunar ta samar da sababbin gidaje ga jami’anta da ke cigaba da yi wa ƙasa hidima da ke matakai daban-daban.
Haka kuma, shugaban rundunar ya amince da sayen rukunin gidaje tare da ƙawata ta musammman ga jami’an da ba su da aure, lamarin da acewarsa zai taimaka wajan ƙara inganta ayyukansu.
