Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe
Yayin da Jihar Gombe ke ƙara azama domin cimma burinta na zama ba tare da fitsari da bayan gida a fili ba (ODF) nan da shekarar 2025, an buƙaci masu ruwa da tsaki su rungumi tsarin sarrafa dattin bayan gida (FSM) domin inganta lafiyar jama’a, tsaftar muhalli da bunƙasa tattalin arziki.
A wani taron wayar da kai da aka shirya wa manema labarai a Gombe, shugabar ofishin UNICEF na Bauchi, Dr. Nuzhat Rafique (wadda Jami’ar WASH ta UNICEF, Nanbam Michael ta wakilta), ta jaddada muhimmancin fara shiri da wuri, tare da buƙatar kafafen yaɗa labarai su riƙa yaɗa labarai kan FSM.
Ta bayyana cewa, da ci gaba da wayar da kan al’umma ta hanyar tsarin Community-Led Total Sanitation (CLTS), akwai yiwuwar wasu al’umma a Gombe za su kai matsayin ODF kafin ƙarshen shekarar 2025.
Farfesa Wilson Ɗanbature daga jami’ar gwamnatin Jihar Gombe ya bayyana irin damar da ke tattare da FSM wajen samar da ayyukan yi, kare muhalli da ƙara samun kuɗaɗen shiga.
Ya buƙaci gwamnati da masu zuba jari su mayar da hankali wajen gina cibiyoyin tace dattin bayan gida (FSTPs) domin ƙarfafa tsarin tsafta da kiwon lafiya.
Shi ma Dr. Abubakar Lumumba daga hukumar RUWASSA ya bayyana cewa har yanzu babu wata al’umma a jihar da aka tabbatar da ta kai matsayin ODF.
Ya ce akwai buƙatar sauya halayen jama’a da goyon bayan masu ruwa da tsaki domin kawar da ɗabi’ar ’ar yin bayan gida a fili.
