Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja
Shugabanni da mambobin ƙungiyar ma’aikatan sufuri ta ƙasa (RTEAN) sun bayyana matuƙar alhininsu dangane da rasuwar tsohon shugaban ƙasar tarayyar Nijeriya, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya.
Shugaban ƙungiyar RTEAN na ƙasa, Dakta Musa Muhammad Maitakobi, ya yi matuƙar alhinin rashin babban jigo, mai kishin ƙasa, kuma shugaba mai gaskiya, riƙon amana, da yi wa ƙasa hidima.
A cikin saƙon ta’aziyyar da mai mataima masa, Muhammad Abubakar Bishara ya sanya wa hannu, ya bayyana marigayi Janar Buhari a matsayin ginshiƙin jagoranci da riƙon amana, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai da ci gaban Nijeriya, inda ya ce sadaukarwar za su dawwama a zukatan al’umma.
Ya kuma yi kira ga miliyoyin ‘yan ƙungiyar RTEAN da ke faɗin ƙananan hukumomi 774 na tarayya da sauran ‘yan Nijeriya da su yi addu’ar Allah ya gafarta masa kurakuransa ya kuma saka masa da gidan aljanna.
