Ziyarar Kano: Tinubu ya yi jimamin rasuwar Ɗantata da yaba wa alkhairansa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A jiya Juma’a ne Shugaba Bola Tinubu ya ziyarci Kano da nufin jajenta wa iyalai gwamnati da ɗaukacin al’umma bisa rasuwar hamshaƙin attajiri Alhaji Aminu Ɗantata.

Ya bayyana mamacin a matsayin mai nagarta da tausayin al’umma wajen inganta rayukansu, yana mai cewa rayuwarsa abin kwaikwayo ne a gare su.

A yayin ziyara Shugaban Ƙasar, ya samu ganawa da mambobin iyalan mamacin jami’an gwamnatin jihar da sarakuna da sauran masu alfarma inda ya yi musu jajen rashin hamshaƙin, wanda ya rasu a ranar 28 ga watan Yuni, 2025 a Dubai bayan shafe shekaru 94 a duniya.

An kuma yi masa jana’iza ne a Madinah, Saudiyya a ranar 1 ga watan Yuli.

Shugaba Tinubu ya labarta kusancin da ke tsakaninsa da marigayin musamman a lokacin da ya kai masa ziyara a shekarar 2023 da ya ke yaƙin neman zaɓe.

Ya ce, Ɗantata mutum be da ya rayu wa al’umma duba da yadda ya sadaukar da dukiyarsa wajen hidimta musu.

Daga cikin waɗanda suka raka Shugaba Tinubu ta’aziyyar akwai Shugaban Majalisar Dattawa da mataimakinsa, wato Godswill Akpabio da Barau Jibrin da ministoci da dama

By Babaji