Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyar Arewa Think Tank (ATT), ta yaba wa shugaban ƙasa Bola Tinubu bisa yi wa marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari jana’izar da ta dace a Daura, jihar Katsina.
Kungiyar ta ce, shugaba Tinubu ne zai gaji ƙuri’un da Buhari ya samu a Arewa saboda a yanzu jama’a sun gamsu cewa za su mayar da shi kan karagar mulki a karo na biyu.
Shugaban ƙungiyar Muhammad Alhaji Yakubu a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce matakin ya nuna yadda shugaba Tinubu ke mutunta magabacinsa da kuma sadaukarwar da ya yi wajen haɗa kan ƙasa.
Yakubu ya yi hasashen cewa shugaba Tinubu zai samu ƙuri’u sama da miliyan 12 daga yankin, inda ya bada misali da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2019 da Buhari ya samu ƙuri’u masu yawa daga yankin arewa.
Shugaban ƙungiyar Arewa Think Tank ya ce jana’iza a jihar ya kasance amincewa da shugabancin shugaba Tinubu, inda ya ƙara da cewa hakan ya nuna cewa yana iya haɗa kan jama’a tare da inganta haɗin kan ƙasa.
Ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su baiwa shugaba Tinubu damar cika alƙawuran da ya cauka da kuma gina kyakkyawar makoma ga kowa.
“Jana’izar ta kasance wata alama ce ta girmamawa da kuma nuna godiya ga gudunmawar da marigayi tsohon shugaban ƙasa ya bayar wajen ci gaban Nijeriya, a bayyane yake cewa za a iya tunawa da abin da Buhari ya gada saboda ƙoƙarin da ya yi na daidaita tattalin arzikin ƙasa, da inganta tsaro, da inganta dimokuraɗiyya.
“Mutanen Arewacin Nijeriya sun yaba da wannan matakin na Shugaba Tinubu kuma za su mayar da martani da ƙuri’unsu a zaɓe mai zuwa.
“Al’ummar Arewacin Nijeriya za su goyi bayan Shugaba Tinubu su mara wa manufofinsa na ci gaban ƙasar nan baya. Don haka muna so mu buƙaci ‘yan Nijeriya su marawa Shugaban ƙasa baya, su marawa ƙoƙarinsa na gina ƙasa mai inganci ga kowa da kowa.
“Idan aka dubi salon jagorancin shugaba Tinubu, ya nuna kansa a matsayin ɗan ƙasa mai mutunta magabatansa domin wannan karimcin da shugaban ƙasa ya yi wa Buhari ya nuna cewa ya jajirce wajen ganin an haɗa kan ƙasa da kuma yadda yake son haɗa kai da wasu domin gina Nijeriya mai inganci,” inji Yakubu.
