Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban kwamitin harkokin cikin gida na Majilisar Wakilai kuma Dujiman Katsina Hon Aliyu Abdullahi ya samar masa 91 aikin yi a mazaɓar sa na ƙananan hukumomin Musawa da Matazu a Jihar Katsina.
Mataimaki na musamman kan yadda labarai na ɗan majalisar Mr Sardauna Francis a wata takardar sanar wa da ya tura wa manema labarai a Katsina.
A makon da ya gudana ɗan majalisar mai wakiltar ƙananan hukumomin Musawa da Matazu ya rabawa matasan yankin takardar kama aiki a yankin.
Takardar aikin ta ƙunshi kama aiki a hukumomin jami’an tsaro da ke ƙarƙashin ma’aikatar harkokin cikin gida na gwamnatin tarayya.
Akwai hukumar shigi da fici, hukumar kashe gobara, hukumar gyaran hali da sauran su.
Dujiman Katsina ya yi alƙawarin ƙara samar ma matasan yankin ƙarin guraben aiki a sauran ma’aikatun gwamnatin tarayya.
Ya nuna gamsuwa ga cigaba da aka samu a fanin tsaro a yankin wanda ya danganta da irin gagarumar gudummawa da gwamnatin Dikko Raɗɗa, haɗin gwiwa da jami’an tsaro ke badawa wajan dawo da zaman lafiya a yankin da jiha baki ɗaya.
