APC za ta maye gurbin Ganduje ranar Alhamis cikin yanayi na tsamari

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyya mai mulki, APC ta shirya gudanar da zaman majalisar zartarwa a ranar Alhamis, 24 ga Yuli, 2025 domin naɗa sabon shugaba, wanda zai maye gurbin Dakta Abdullahi Umar Ganduje a muƙamin.

Za a gudanar da zaman ne a Abuja, wanda zai samu halartar jiga-jigan jam’iyyar a yayin da aka samu rabuwa tsakanin jagororin game da al’amarin.

Tun bayan da Ganduje ya yi murabus a watan Yuni, APC ta naɗa Ali Bukar Dalori a matsayin shugaba na riƙon ƙwarya.

Akan haka ne aka samu rabuwar kai game da ko Dalori ne wanda zai zama shugaban jam’iyyar na dindindin ko kuma a canza shi.

A yayin kammala shirye-shiryen zaman majalisar ne aka fitar da sunayen mutane biyu da ake ganin ɗayansu ne ka iya samun muƙamin.

Na farko shi ne tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Umar Tanko Al-Makura da kuma Farfesa Nentawe Yiltwatda, wanda shi ne Ministan Jin-ƙai na yanzu.

Duba da bin tsarin karɓa-karɓa da bada gudunmuwa a jam’iyyar, hakan ya sa aka zaɓo mutane biyun daga shiyya guda, wato Arewa ta Tsakiya.

Tun a watan Yuli, 2023 ne shiyyar ta rasa muƙamin, a lokacin da tsohon shugaban jam’iyyar, Abdullahi Adamu ya yi murabus, lamarin da ya sa Ganduje ya maye zama shugaba.

By Babaji