Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Rayuwar duk wani taliki na kan ƙa’idar ƙarewa wata rana kuma hakan ne ya yi ta faruwa tun tsawon tarihin halitta. Mutum na farko wato Annabi Adamu alaihis salam ya bar duniyar nan. Duk wani mai daraja zai bar duniya. Mu tuna mafi darajar halitta Annabi Muhammadu mai tsira da aminci shi ma ya yi wafati. In haka ne ai kowa ma na da iya shekarun da zai yi a doron ƙasa sannan ya ɗanɗani mutuwa! Marigayi mai waƙa Alhaji Adamu ɗan Maraya Jos na cewa “mutuwa rigar kowa..da da hali da ya tuɓe..amma babu hali” kuma hakan ya tabbata don ɗan Maraya ya rasu shekarun baya. Mutuwa tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ta zo ba tare da tsammanin hakan ba. Wannan kuwa don dama an saba sanin ko jin yadda marigayin kan tafi Landab don neman magani musamman daga lokacin da ya hau kujerar shugabancin Nijeriya tsakanin shekara ta 2015-2023. Akwai wata doguwar jinya da marigayin ya yi inda ya zauna a asibiti a Landan wajen wata 3 amma Allah cikin ikon sa ya dawo ya cigaba da mulkin sa. A wancan lokacin jama’ar ƙasa sun yi ta yi ma sa addu’ar Allah ya ba shi lafiya kuma Allah ya amsa addu’ar ya ba shi sauƙi ya dawo Abuja. ƙasa ta ɗau murna bisa amsa addu’ar da Allah maɗaukakin sarki ya yi wajen ba wa wannan bawan na sa da ‘yan ƙasa ke kyautatawa zaton zai yi jagoranci mai adalci da zai bunƙasa rayuwar talakawa. Haƙiƙa Allah ya ba wa marigayi dammar yin shugabanci na wa’adi biyu tsawon shekaru 8 inda bayan sauka daga karaya da kimanin shekaru biyu da wata ɗaya da kwanaki Allah ya karbi abun sa. Labari daga wajen ɗan uwan sa Malam Mamman Daura marigayin ya ma samu sauƙi kafin ciwon ya sauya kala inda hakana ya zama ajali. Ita cutar ajali wani loakcin ta na da irin wannan yanayi na mai jinya zai samu sauƙi har ma ya yi magana da dammar aikawa da saƙonni ko yin wasiyya inda daga bisani sai ciwo ya dawo shikenan sai rai ya yi halin sa. A labarin da a ka samu ta hanyar matar sa Aisha, marigayin ya ba ta saƙon ta buƙaci ‘yan Nijeriya su yafe ma sa gabanin a kai shi kabarin sa.
Wanda ya yi mulkin ƙasa irin Nijeriya kuma ga ma irin shugaban da a ke kyautatawa zato zai taɓuka abun kirki ba zai zama abun mamaki ba a samu ra’ayoyi mabambanta game da shi. Abun da ya zama rinjaye shi ne akasarin jama’a na nuna juyayi kan rasuwar Janar Buhari kuma har ma da ambata cewa sun yafe ma sa laifukan da su ke ganin ya aikata mu su musamman ga rashin samun muradun da su ka sa ran samu lokacin da ya hau madafun iko. Ba mamaki lura da irin haka na samuwar waɗanda su ka samu sanyin guiwa kan yanayin mulkin sa, marigayi Buhari ya fito ya nemi afuwar su ya na mai tabbatar da cewa akwai waɗanda zai yiwu ya mu su ba daidai ba don haka ya na neman su yi haƙuri su yafe. Ga al’ummar arewacin Nijeriya da dama marigayin ne gwanin su, da yawa sun shiga damuwa kan yadda gwamnatin ta sat a rufe kan iyaka da hakan ya dakatar da hada-hadar kawo kayan masarufi musamman abinci. Rashin shigowar abinci ya haddasa tashin farashin kayan abincin ba ma irin shinkafa. Lokacin da jama’a da dama ke ƙorafi su kuwa manoma shinkafa farin ciki su ke yi don hanyar arzikin su ta buɗe. Marigayin ya ba da dalilin ɗaukar matakin ne don a riƙa noma abinci a cikin gida. An noma abincin amma ba mamaki saboda rashin isar tallafin gwamnati ga harkar noman ya sa kayan da a ka noma su ka zama da dan karen tsada. Ga kasa gaba daya yanda a ka riƙa samun hauhawan farashin man fetur ya jawo damuwa ainun da jefa al’umma cikin ƙunci duk da ma ashe a lokacin ba a gama cire dukkan tallafin man ba kenan. A karshen mulkin sa gabanin zaɓen 2023 marigayi ya kawo wani tsari na canja kuɗi inda hakan ya kawo ƙarancin takardun kuɗi a tsakanin jama’a. Wannan ya haddasa matsaloli da yawa kuma ba a samu sa’ida ba sai da kotun ƙoli ta yanke hukunci kan amfani da sabbi da kuma tsoffin kuɗi. Bayan an farfaɗo daga matsalar marigai Muhammadu Buhari ya bayyana cewa an dau matakin ne don hana ‘yan siyasa sayen ƙuri’a a babban zaɓe. Shin ‘yan siyasar sun sayi ƙuri’ar ko hakan ya daƙile su daga samun dammar saya don haddasa maguɗin zaɓe, an dai gudanar da zaɓen kuma jam’iyyar APC ta marigayin ta zarce da mulki ƙarƙashin shugaban da ke gado yanzu wato Bola Ahmed Tinubu.
Sauran duk wani zance ko karafi ya zama tarihi. Haka manufofin gwamnati su ke ko sun yi wa ‘yan ƙasa daɗi ko ba su yi ba zai hana gwamnatin ɗaukar matakan da ta ke ganin su ne mafi a’ala ga kasa ba. Abun da talakawa su ka fi tsammani ga gwamnatin marigayin da su ke ɗauka gwamnatin su ce, in sun yi ƙorafi ta saurara kuma ta biyewa buƙatun su. Duk yanda mu ka dau lamarin gwamnati ya iya wuce tunanin mu. Mulki musamman a irin Nijeriya tamkar kokwa inda na bayan fage a kan ce shi ne gwani don ba mamaki ya na ganin da an yi haka sai ka ga an samu nasara. Mu jama’ar kasa mu na waje mu na duba abubuwan da gwamnati ke yi kuma ƙalilan ne daga cikin mu ke da sahihan bayanan gaskiya na abun da ke faruwa ko dalilan da su kan kawo kwan gaba kwan baya. Waɗanda su ka jajirce ga ba wa marigayi uzuri su ne waɗanda ke cewa rashin lafiya ta hana shi yin mulki tamkar yanda a ka yi tsammani. Shi kuma marigayin kan nuna kamar ba mai yiwuwa ba ne ya tabuka yadda ya yi a mulkin soja don lokacin da kuruciya kuma ai soja kan yi aiki ne da dokar soja ba ya amfani da tsarin mulki. A dimokraɗiyya ya zama wajibi shugaba ya riƙa aiki da majalisar dokoki. Farkon mulkin Buhari an a za samun tafiyar hawainiya ga rashin jituwa tsakanin fadar gwamnati da majalisar dokoki ƙarƙashin sanata Bukola Saraki don yanayin yadda shugabancin majalisar ya zo ba tare da goyon baya ko amincewar sashen zartarwa ba. An yi ta matakai na neman tsige Saraki amma hakan ya ci tura har ya kamala jagorancin sa a 2019. Dagan an an samu majalisa da ta tafi da fadar gwamnati kusan 100/100 ƙarƙashin sanata Ahmed Lawan. ‘Yan Nijeriya su ne shaida shin an samu nasarar cimma muradun gwamnatin talakawa ko kuwa a’a. Nan dai har marigayi ya samu ya kamala wa’adin say a mika ragama ga sabon shugaba Tinubu a ranar 29 ga Mayu 2023. An san dai babu batun tallafin man fetur a kasafin kuɗi na wannan shekarar amma tsohuwar gwamnati ta bi hanyoyi irin na ta har ta sauka ba ta kammala janye tallafin ba. Ilai kuwa a nan wajen karbar mulkin sabon shugaba Tinubu ya aiyana cewa tallafin man fetur ya tafi! Daga nan dai kowa ya san yanda ƙasar ta shiga inda farashin kayan masarufi ya kara cillawa sama. Gaskiyar magana talakawa sun kara shiga matsalar rayuwa amma in an duba duk manyan ‘yan takara na adawa ma sun yi alwashin cire tallafin in an zabe su. Bambancin da masu sharhi ke magana a kai shi ne shin janyewar a jawabin farko da shugaba Tinubu ya yi haka ma sauran za su iya yi ko sai an dan tafi kadan a rika janyewa a hankali har a kamala gaba ɗaya? Koma yaya mu ka kalli wannan al’amari ya dace gwamnati ta dimokraɗiyya ta rika sara ta na duba bakin gatari don kar a a wayi gari kukan jama’ar ƙasa ya fi murmushin su yawa.
Marigayi shugaba Muhammadu Buhari dai ya tabbata cewa ya na da takatsantsan da dukiyar jama’a wato kai tsaye ba za a iya zargin sa da tara abun duniya ba amma ba mamaki wasu muƙarraban sa sun hana nasarar wannan yanayi na riƙon amana da kau da kai daga tara dukiya. An sha mamaki yanda hukumar yaƙi da cin hanci EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan babban banki Godwin Emefiele da zargi na mummunar badaƙala da ya aikata ƙarƙashin mulkin marigayi Buhari. Ta yiwu akwai waɗanda a gwamnatin Buhari ke amfana da Emefiele da hakan ya sa ko bayan kamala wa’adin mulkin sa a ka sabunta ma sa wani wa’adin. Mafi mamakin ma gwamnatin ta gaje shi ne daga tsohuwar gwamnatin Goddluck Jonathan da ta zarga da badaƙala. Akwai wasu misalan da ke nuna Buhari dai ya zuba ido don ɗabi’ar wasu daga makusanta kan iya sabawa da aƙidar sa amma ba zai iya hukunta su ba don shekaru sun ja ba kamar yanda ya ke a mulkin soja shi da marigayi Tunde Idiagbon ba.
KAMMALAWA
Duk mai rai mamaci ne don haka a kyautata harshe ga wanda Allah ya karɓa da yi ma sa fatar samun rahama daga Allah. Dukkan mu wataran hanyar da ya ce. Allah ya sa mu gama da duniya lafiya. Daga dawowa mulkin Buhari bayan shekara 30 da barin madafun iko na soja shekara 10 ne cif hakanan ya kasance a tsawon shekaru 20 cikin dimokraɗiyya duk zaɓe akwai sunan marigayin kan katin kaɗa ƙuri’a! yau kuma marigayi na gidan gaskiya da ke jiran duk mai rai!
