Ana zargin jami’in hukumar gidan gyaran hali ta Nijeriya da kashe ɗan jarida mai ɗaukar hoto a Jihar Kogi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani jami’in hukumar da ke kula da gidajen yari mai suna Adebayo Pelumi ya kashe wani ɗan jarida mai ɗaukar hoto Ayo Aiyepeku a jihar Kogi.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa wanda ake zargin ya gudu, inda ya bugi marigayin a kai, sannan ya yanka shi ya sanya sassan jikinsa a cikin firiji.

Lamarin ya faru ne a ofishin mamacin da ke kusa da unguwar gwamnati (GRA) a Lokoja, jihar Kogi.

Wanda ake zargin da ya gudu yana aiki ne da Zone H da ke Makurdi, wanda ya haɗa da jihar Kogi da Binuwai.

Wani ganau ya ce, “Lokacin da muka gano an kashe Adebayo Pelumi tare da daddatsa gawarsa, nan take muka sanar da ‘yan sanda kuma suka fara bin sawun wanda ake zargin.”

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi (PPRO) ya tabbatar wa Manhaja faruwar lamarin a ranar Laraba.

“An kai rahoto ga jami’in ‘yan sanda na Dibision A kan kisan da aka yi wa Ayo, wanda laifin kisan kai ne, bayan sun shigar da ƙarar ne ‘yan sandan suka ɗauki matakin zuwa wurin, aka fara bincike.

“Kwamishanan ‘yan sanda CP Miller Dantawaye ya bai wa DPO umarnin miƙa lamarin zuwa CID na jihar domin su ne suke gudanar da al’amuran da suka shafi kisan kai domin gudanar da bincike na gaskiya, ana ci gaba da ƙoƙarin ganin wanda ake zargin wanda a halin yanzu bai shiga hannu ba, za a kama shi kuma a gurfanar da shi a gaban kuliya.”

By ukarofi