
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wata Babbar Kotu a Jihar Akwa-Ibom ta yanke wa wasu ƴan fashi guda biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun su da laifin fashi ga wasu ƴan adaidaita sahu a babban birnin jihar, Uyo.
Ɗaya daga cikin su shi ne Lance Corporal Promise Okokon Usoro, wanda tsohon soja ne da aka sallame shi a aiki daga bataliya ta 6 ta rundunar sojojin Nijeriya dake Barikin Ibagwa a Ƙaramar Hukumar Abak.
Usoro mai shekaru 41, an same shi ne da bindiga ƙirar AK-47 da laifin yin fashi ga wani mai suna Peter Daniel Okon inda ya ƙwace masa babur ɗinsa mai taya uku bayan yi masa barazana da bindiga a daren ranar 10 ga watan Fabarairun 2013.
Da fari, an same shi ne da laifin saɓa wa aikin soja, lamarin da ya sa aka sallame shi a aiki tare da damƙa ga ƴan sanda domin gurfanar da shi a kotu.
Tuni Usoro ya masa laifin yin fashi sau uku ga masu adaidaita sahu a birnin Uyo tare da taimakon wani da ake kira da JJ wanda shi ma a yanzu yana hannu.
