Rundunar ‘yan sandan Katsina ta tallafa wa jami’anta da suka rasu da Naira miliyan 11

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kusan Naira miliyan 11 aka bai wa iyalan jami’an ƴan sanda 34 da suka rasa rayukansu a lokacin gudanar da aikin su.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya faɗi haka a wata takardar sanarwa da ya rabawa manema labarai a Katsina.

Ya ce shi wannan tallafin kuɗi na cikin ƙarƙashin shirin tallafawa iyalai na shugaban yan sanda na ƙasa da inshuwara ga iyalan mamatan.

Mataimakin Kwamishinan ƴan sanda mai kula da sashin kuɗi Aminu Usman Gusau ya wakilci kwamishinan ƴan sanda Bello Shehu wajan bikin bada tallafin a hedkwatar ƴan sanda a Katsina.

Kwamishinan yan sanda Bello Shehu ya yabawa shugaban ƴan sanda na ƙasa bisa nuna tausayawa da jajircewa wajen inganta rayuwar ƴan sanda da iyalan su.

Ya tunatar da iyalan mamatan da su ɗauki wannan tallafi a matsayin taimakawa ga waɗannan jarumai da su ka rasa rayukansu wajen kare rayukan al’umma.

CP Bello Shehu ya shawarci iyalan da suka amfana da wannan tallafi da suyi amfani da kuɗin wajen inganta rayuwar iyalansu.

Da yake magana a madadin iyalan ƴan sandan da suka amfana da tallafin Nuhu Bello Goge ya miƙa godiyar su ga shugaban ƴan sanda na ƙasa da cp Bello Shehu da suka taimaka wajen samun tallafin.

Ya kuma tabbatar masu da cewa zasu yi amfani da wannan tallafin kuɗin wajan kula da iyalan su.

By ukarofi