
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar APC da su warware matsalolin ci-gaba da al’umma suke fuskanta a jihohinsu.
A lokacin da ya ke magana taron kwamitin zartarwar jam’iyyar (NEC)a Fadar Shugaban Ƙasa, Tinubu ya ce har yanzu ƴan Nijeriya suna fama da tsananin rayuwa da cigaban da nuna rashin gamsuwa da salon tafiyar mulkinsu.
Ya ce, akwai buƙatar gwamnonin su mayar da hankali wajen inganta rayukan al’umma tun daga matakin ƙauyuka ta yadda za a samu sauƙi halin matsalolin da suke fuskanta.
Ya jaddada cewa ƙofa a buɗe ta ga waɗanda ke son shiga jam’iyyar APC don ganin an dama da kowane ɓangaren ƙasa.
Ya kuma kirayi Shugaban jam’iyyar da ya samar da kwamitin ayyuka da zai ziyarci jihohi tare da tabbatar da tantance mambobin jam’iyyar.
