
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Juma’a Shugaba Bola Tinubu ya yi magiya ga kamfanonin raba wutar lantarki (GenCos) kan su bai wa Gwamnatin Tarayya ƙarin lokacin tantance bashin da aka riƙe musu na tsawon lokaci.
A yayin ganawa da ƙungiyar kamfanonin ƙarƙashin jagorancin Kanal Sani Bello a Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja, Tinubu ya tabbatar musu da cewa gwamnatinsa tana aiki tuƙuru wajen ganintq warware matsalolin kuɗaɗe da fannin wuta ke fuskanta.
Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa Shawara kan harkokin makamashi, Olu Verheijen ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya amince da ware tiriliyan N4 ga shirin magance matsalolin kuɗi da fannin ya ke fuskanta.
Shugaba ƙasar ya kuma yi nazari game da bashin da fannin ke bi tun daga zamanin gwamnatocin baya, yana mai cewa zai tabbatar da gaskiya da adalci wajen warware su.
Ya kuma ce, akwai buƙatar kamfanonin da cibiyoyin kuɗi su yi haƙuri a yayin da hukumomin gwamnati da ɓangaren shari’a suek gudanar aiki akan al’amarin.
Tinubu ya ƙara da cewa, a yayin da aka yi watsi da ƙoƙarin da fannin ke yi a baya, a yanzu gwamnati tana mayar da hankali a kai yadda ya dace.
