Manoma sun koka kan tsadar taki a Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Rahotanni daga jihohin da ke samar da yawancin kayan amfanin gona sun tabbatar da cewa manoma na barin shukan masara da shinkafa saboda tsadar takin zamani.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya ke cewa ta raba takin zamani kyauta ga manoma.

Manema labarai sun tattauna da manoma da sauran masu ruwa da tsaki domin jin halin da suka shiga kan tsadar taki a bana.

Wasu daga cikin manoman sun bayyana cewa, yanzu haka ba za su iya sayen buhun taki ba saboda hauhawar farashin sa wanda ya kai sama da N50,000 a wasu kasuwanni.

Yayin da ake fargabar ƙarancin abinci a Nijeriya, manoma da dama na komawa shuka gero, dawa, wake da kuma kayan lambu waɗanda ba sa buƙatar takin sosai.

Bincike ya gano cewa manoma da dama sun daina shuka masara da shinkafa, su na komawa kayan lambu kamar albasa da tattasai.

Malam Hamza Adamu daga ƙaramar hukumar Igabi a Kaduna ya ce, ba zai iya ci gaba da shuka masara ba.

Ya ce, “Ba za ka iya sayen buhun taki da kuɗin da za ka sayar da buhun masara ba. Kuma idan ka shuka ba tare da taki ba, to za ka gamu da matsala sosai.”

A cewar wani bincike, buhun taki nau’in Urea yanzu ya kai tsakanin N47,000 da N50,000, yayin da NPK ke kai N55,000, lamarin da ya sanya manoma da dama hakura da shuka masara.

Wani manomi, Bello Idris Dalleje, ya ce: “Buhun Urea yanzu ya kai N50,000, amma buhun masara yana kasa da N38,000. A haka ba za ka iya samun riba ba.”

Ya ƙara da cewa, sau da dama gwamnati na cewa ta raba taki, amma, “Ana cewa manoma hudu su raba buhu daya, wanda hakan manomi ɗaya ke buƙata a gona ɗaya.”

Shugaban ƙungiyar Manoman Masara (MAAN) reshen Jihar Kaduna, Mohammed Kabir Salihu, ya tabbatar da cewa manoma na barin shuka masara saboda tsadar taki da kuma faɗuwar farashi.

Ya ce, “Yawancin manoma yanzu sun koma shuka albasa, tattasai da sauran kayan lambu saboda suna buƙatar taki kaɗan.”

Salihu ya zargi shigo da masara daga ƙasashen waje da faɗuwar farashinta da sanya manoma shan wahala.

Shugaban ƙungiyar Manoma ta ƙasa (AFAN), Kabiru Ibrahim, ya ce tsadar taki barazana ce ga ƙoƙarin ƙasar wajen cimma wadatar abinci.

Ya ce: “Yawancin ƙananan manoma da ma manyan manoma na fama da tsadar taki, wanda hakan ke barazana ga samar da wadataccen abinci a Nijeriya.”

By ukarofi