NAPTIP ta gargaɗi iyaye kan barin ’ya’ya sakaka

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugabar Hukumar Yaƙi da Fataucin Bil Adama ta ƙasa (NAPTIP), Binta Adamu Bello, ta gargaɗi iyaye da su guji barin yara a hannun mutanen banza, makwabta marasa amana, inda ta ce irin waɗannan na iya sanya yara cikin mawuyacin hali na fataucin mutane da sata.

Ta bayyana hakan ne a lokacin da ta haɗa wata yarinya ’yar shekara biyar da aka yi safararta mai suna Rahama Ibrahim da iyayenta a Damaturu, jihar Yobe, ranar Juma’a.

Jami’in Yaɗa Labarai na NAPTIP, ɓincent Adekoye, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce shugabar ta samu wakilcin Saleh Zakar, kwamandan hukumar a jihar Yobe.

A cewar sanarwar, an sace Rahama ne a Damaturu watannin baya bayan wani direba da ake zargin yana da hannu wajen satar yara amma jami’an tsaro na farin kaya (DSS) suka kama wanda ake zargin a Abuja. An gurfanar da shi a gaban kotu.

“An gudanar da taron ne a gidan gwamnati da ke Damaturu a gaban mataimakin gwamnan jihar, Hon. Idi Barde Gubana, tare da haɗin gwiwar jami’an DSS na jihar Yobe,” inji sanarwar.

Da yake jawabi bayan karɓar yarinyar, mahaifinta, Malam Ibrahim, ya bayyana godiyarsa ga Shugabar Hukumar NAPTIP bisa ƙoƙarinta na tabbatar da isasshen kulawa ga yarinyar.

A nasa jawabin, Gubana ya yabawa hukumar ta NAPTIP bisa yadda take gudanar da ayyukan yaƙi da fataucin yara tare da samun nasarar dawo da yarinyar tare da ba hukumar tabbacin goyon baya daga gwamnatin jihar Yobe.

By ukarofi