Sama da mutum miliyan 3.7 ke fuskantar yunwa a Arewa maso Gabashin Nijeriya – ICRC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar Ba Da Agaji ta ƙasa da ƙasa ta Red Cross ta koka kan ƙaruwar yunwa a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya, inda sama da mutane miliyan 3.7 ke fuskantar ƙarancin abinci a halin yanzu.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, ƙungiyar ta ce, yawancin waɗanda abin ya shafa manoma ne da a da su ke ciyar da al’ummarsu amma a yanzu su na fafutukar rayuwa.

Rikicin da aka kwashe shekaru ana yi ya raba iyalai da muhallansu, da rashin samun filayen noma, da kuma kawo cikas ga samar da abinci a cikin gida.

Tun bayan ɓarkewar tarzoma da ‘yan bindiga a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, manoma da dama ne aka tilastawa barin gonakinsu a yankunan karkara.

Har ila yau, rashin tsaro ya haifar da raguwar ayyukan kamun kifi, musamman a kewayen tafkin Chadi da manyan koguna.

Hanyoyi na makiyaya da wuraren kiwo na gargajiya sun lalace sosai, lamarin da ya shafi rayuwar waɗanda suka dogara da kiwon dabbobi.

Sakamakon haka, a yanzu da yawa daga cikin manoma a jihohin da abin ya shafa sun dogara ne kacokan kan tallafi daga gwamnati, ƙungiyoyi ko ɗaiɗaiko mutane.

Wannan abu da ya taɓarɓare ya haifar da ƙaruwar bautar da yara, rashin zuwa makaranta, da auren wuri a yankin Arewa maso Gabas, musamman a yankunan da ake fama da rikici.

Sanarwar ICRC ta ruwaito Modu Umar, wani shugaban yankin Dikwa, yana mai cewa, “A yanzu haka, muna fuskantar matsananciyar aarancin abinci, wasu iyalai su na tafiya mai nisa a kowace rana don tattara itacen da za su sayar, don kawai su samu abinci, noma ne kawai mafita ga yunwar.

ƙungiyar ta kuma ce rashin tsaro ya sa noma na yi wa manoma matuƙar wahala.

An ruwaito Churi Ibrahim, wani dattijo mai shekaru 70 daga Gajibo, ya ce, “Wasu mutane na tafiyar sa’o’i uku don isa gonakinsu, da zarar ka isa gonar ka, ka riga ka gaji, kuma kafin ka dawo gida dare ya yi”

Sanarwar ta kuma yi nuni da cewa, duk da haɗarin da ke tattare da hakan, manoman sun ƙuduri aniyar ci gaba da noma a gonakinsu.

Bintu Konto, wata uwa mai yara biyar, a cewar sanarwar, ta ce, “Ko da kun ji tsoro, dole ne ku je, idan ba ku yi noma a lokacin damina ba, ba za ku ci abinci ba.”

Shugabar ofishin ICRC a Maiduguri, Diana Japaridze, ta nakalto a cikin sanarwar, ta ce farkon lokacin bazara yana ƙara matsi yayin da kayan abinci ke raguwa.

“Wannan shi ne lokacin da mutane ke shan wahala wajen sayen abinci, inda yawancin iyalai da rikici ya shafa ba za su iya biyan kuɗi mai yawa ba. An tilasta musu su iyakance yawan abincinsu,” inji Japaridze, ta ƙara da cewa rikicin ya haifar da hauhawar rashin abinci mai gina jiki, musamman a tsakanin yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar da masu juna biyu ko masu shayarwa.

Hakazalika, rahoton Cadre Harmonise, wanda Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar ɗinkin Duniya (FAO) na Majalisar ɗinkin Duniya da abokanan hulɗar samar da abinci suka fitar watanni da suka gabata, ya yi hasashen za a fuskanci matsalar abinci da sinadari mai gina jiki a faɗin Nijeriya.

A cewar rahoton, kimanin mutane miliyan 30.6 a cikin jihohi 26 da babban birnin tarayya Abuja na iya fuskantar matsananciyar rashin abinci da abinci mai gina jiki a lokacin rani na watan Yuni zuwa Agustan 2025.

Kayayyakin abinci su na raguwa a lokacin rani, wanda kuma aka sani da lokacin girbi, wanda ke haifar da hauhawar yunwa da rashin abinci mai gina jiki, musamman a yankunan karkara.

A Nijeriya, lokacin bazara yakan kai daga watan Mayu zuwa Satumba, inda jihohi kamar Borno, Adamawa, da Yobe suka fi fama da matsalar.

Tun da farko dai Majalisar ɗinkin Duniya ta nuna damuwa game da yiwuwar samun taɓarɓarewar al’amuran jinƙai, musamman dangane da raguwar kuɗaɗen agaji da aka samu a baya-bayan nan.

A yayin fitar da rahoton Cadre Harmonise a Abuja, Dominiƙue Koffy Kouacou, wakilin FAO a Nujeriya da ECOWAS, ya buƙaci gwamnatin Nijeriya, masu ba da taimako, da masu ruwa da tsaki da su ɗauki matakin gaggawa, da samar da kayan aiki, da aiwatar da manufofi don hana ci gaba da taɓarɓarewar lamarin.

Ya ce, akwai buƙatar a gaggauta tallafa wa ɓangarori daban-daban a faɗin ƙasar nan, musamman a yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, waɗanda ke fama da matsalar ƙarancin abinci da abinci mai gina jiki.

Hakazalika, Cristian Munduate, Wakilin UNICEF a Nujeriya kwanan nan, ya bayyana lamarin a matsayin “mai ban tsoro” tare da bayyana “buƙatar gaggawar ɗaukar matakin haɗin gwiwa don magance taɓarɓarewar rashin abinci da abinci mai gina jiki da ke shafar miliyoyin yara da iyalai masu rauni a faɗin Nijeriya.”

ICRC ta ce, tana tallafawa cibiyoyin daidaita matsalar rashin abinci mai gina jiki da ilimantar da al’umma don taimakawa iyalai kula da yara masu rauni.

ƙungiyar, a cikin sanarwar ta, ta ce ta fara shirin bayar da tallafin noma da ke tallafa wa noman damina da rani, inda ta ce a bana, fiye da gidaje 21,000 manoma ne suka samu iri da suka dace da yanayin gida, tare da kayayyakin shuka domin rage nauyin aiki da kuma inganta noman yadda ya kamata.

“Tallafin ya haɗa da gonaki da kayan lambu, irin su shinkafa, masara, tumatir da kuɓewa, su na ba da gudunmawa ga bambancin abinci da darajar abinci mai gina jiki. Ana kuma horar da manoma kan ayyukan noma mai ɗorewa, su na taimakawa wajen gina ƙarfin gida da kuma tabbatar da cewa za su iya ci gaba ko da lokacin da ICRC ta tafi,” inji sanarwar.

Tare da haɗin gwiwar hukumar noma ta ƙasa (NASC), ICRC ta ce ta kammala gyare-gyare ga wata muhimmiyar hanyar ruwa domin tabbatar da ci gaba da samun ruwan sha ga majalisar gwajin iri da wuraren da ake noma.

Da aka tuntuɓe shi don jin ta baƙinsa kan sabon rahoton ICRC, Darakta-Janar na ƙungiyar gwamnonin Arewa maso Gabas, Umar Musa Gulani, ya ce yana buƙatar lokaci domin ya samu tare da duba rahoton kafin ya amsa tambayoyin da ’yan manema labarai.

“Muna aiki kafaɗa da kafaɗa da ICRC, kuma ina da hanyar samun rahoton kai tsaye daga wajensu domin tabbatar da sahihancinsa.

“Majalisar ba ta karɓe shi a hukumance ba, don haka muna buƙatar lokaci don yin nazari da tattaunawa. Da zarar an yi haka, za mu dawo gare ku,” inji shi.

By ukarofi