Miji ya biya N3m na fansar matarsa da ta yi ƙaryar an yi garkuwa da ita

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jami’an ƴan sanda a Jihar Delta, sun yi nasarar kama wata mata bayan ta yi ƙaryar an yi garkuwa da ita, lamarin da ya tilasta wa mijinta biyan Naira miliyan 3 a matsayin kuɗin fansa.

Lamarin ya auku ne a Asaba, babban birnin jihar, inda aka gano cewa matar, mai shekaru 29, ta karɓi aron N3m ne daga hannun ɗan uwanta da nufin sayan babur mai taya uku, kamar yadda ta shaida wa ƴan sanda.

Saidai hakan bai faru ba domin ta sauya akalarsu wajen sanya su a hidimar aurenta da aka gudanar a watan Maris, 2025.

Ta bayyana cewa, hanya ɗaya da ta ke da ita na ta mayar da kuɗaɗen ita ce ta yi ƙaryar garkuwar, lamarin da ya sa ta haɗa kai da wani mai gadi daga tsohon wajen aikinta.

Kakakin ƴan sandan jihar, SP Bright Edafe ya ce matar ta kira mijin nata a waya ta ce masa tana hanyar dawowa, sai daga bisani aka kira shi aka ce masa an yi garkuwa da ita.

Haka kuma, matar ta ce bayan an tura musu kuɗaɗen ta bai wa waɗanda suka taimaka mata N500,000 yayin da ta riƙe sauran.

A yanzu haka an kama baki ɗaya waɗanda ke da hannu a lamarin kuma ana gudanar da bincike akansu.

By Babaji