Wararrun ‘Yan Majalisar Zamfara za su binciki yadda gwamnatin ke cire kuɗaɗen ƙananan hukumomi

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Wararrun ‘Yan Majalisar Jihar Zamfara ƙarkashin jagorancin Kakakinta Hon. Bashir Aliyu Gummi sun duƙufa wajen bincikar yadda ake ci gaba da cire kashi 3% daga cikin kuɗaɗen da ake bai wa ƙananan hukumomi 14 da aka ware domin ɗaukar nauyin kuɗin jami’ar Jihar Zamfara, dake Talata Mafara.

Hon. Nasiru A. Maru ya bayyana haka a cikin wani ƙudiri da ya gabatar a gaban majalisar a zamansu da aka gudanar a Gusau yau Talata.

A cewar sa, cire kuɗaɗen ya haramta, kuma ya saɓawa ƙa’ida, yana mai cewa kuɗaɗen ƙananan hukumomin an basu ne domin samar da ababen more rayuwa ga jama’a a matakin yankunan karkara.

Sai dai kuma Hon. Aminu Ahmad Keta a wani ƙuduri na daban da ya gabatar a gaban majalisar ya buƙaci gwamnatin Jihar Zamfara da ta biya albashin ma’aikatan da ta dakatar da albashinsu waɗanda suka yi zanga-zanga hanasu albashi tsawon watanni shida, tare da yin kira da a gaggauta mayar dasu aiki.

Majalisar ta kuma bayyana a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, yadda gwamnatin jihar ke tafiyar da al’amuran atsalar rashin tsaro ƙarƙashin jagorancin gwamnatin Gwamna Dauda Lawal a jihar duk da alƙawuran da ya yi na kawo ƙarshen kashe-kashen gilla da masu aikata miyagun laifuka ke yi shekaru biyu da suka gabata.

Majalisar ta yi Allah wadai da kashe mutane 38 daga cikin 56 da aka yi garkuwa da su watanni huɗu da suka gabata daga ƙauyen Banga dake ƙaramar hukumar Ƙaura Namoda da aka yi musu yankan rago tare da nuna alhinin su bisa yadda Gwamna Dauda Lawal ya yi watsi da su ga makomarsu a hannun ‘yan ta’adda tun bayan da akayi garkuwa dasu.

Shima da yake gabatar da al’amarin dake damun al’umma cikin gaggawa a zauren majalisar ɗan majalisar mai wakiltar mazaɓar Ƙaura Namoda ta Arewa, Honarabul Mukhtaru Nasiru Kaura, ya ce ƙaramar hukumarsa na fuskantar hare-haren ‘yan ta’adda inda ya koka da yadda gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ke nuna halin ko in kula kan lamarin.

“Na yi kiraye kiraye da yawa ga gwamnatin jihar kan aiyukan ‘yan ta’adda a Ƙaramar hukumar ƙaura Namoda amma gwamnatin Jihar tayi kunnen uwar shegu har ya kai ga kisan gillar da aka yi wa mutane 38 a baya-bayan nan. Yace

‘Yan majalisar sun yi kira ga gwamnatin jihar Zamfara da ta biya diyya ga iyalan dukkan mutane 38 da aka kashe ba tare da ɓata lokaci ba, tare da jaddada cewa ya isa hakanan dangane da kisan gillar da ‘yan bindiga ke yiwa fararen hula a jihar.

By ukarofi