Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A wata sanarwa ɗauke da sa hannun kwamishinan yaɗa labarai da al’adu Dr Bala Salisu Zango ya bayyana cewa an zaɓi cibiyoyin kiwon lafiya guda biyar da aka keɓe za a fara bada maganin.
Cibiyoyin kiwon lafiya guda biyar da aka zaɓa sune babban asibitin Katsina, babban asibitin ƙwararru na Amadi Rimi Katsina, asibitin Turai Yar’adua , babban asibitin Jibia, da babban asibitin Funtua.
kwamishinan ya bayyana cewa hukumar kula da ayyukan kiwon lafiya ta Jihar Katsina, ta sanar da cewa cutar typhoid ya fi tsananta a ƙananan hukumomin Katsina, Kaita, Batsari, Jibia, da Funtua.
Ya ce su waɗannan ƙananan hukumomi an keɓe su a matsayin yanki mai haɗari
“Amma a yankin Daura rahotannin da aka samu da sauƙi,” inji Dr Bala Zango.
Kwamishinan ya jaddada cewa gwamnatin jihar za ta yi duk abinda ya kamata na ganin maganin ya isa kowanne babban asibiti da ke jihar.
