‘
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A ƙokarin da ta ke na yaƙi da ta’addanci, ‘yan sanda sun sami nasarar ceto mutane 28 da ga hannun ‘yan bindiga a ƙaramar hukumar Sabuwa.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya sanar da haka a wata takarda da ya rabawa manema labarai a Katsina.
Ya bayyana cewa wani matashi ya kwarmatawa ofishin ‘yan sandan yankin cewa ‘yan bindiga ɗauke da mayan bindigogi sun tare hanyar Sabuwa zuwa kaya daidai kwanar Inno,inda suka tafi da mutane 14.
DSP Sadiq ya ce nan take DPO da mutanen sa suka tunkari wurin, bayan an daɗe ana ɗauki ba daɗi ‘yan sandan suka sami nasarar ceto mutane 14 sai dai yan bindigan sun kashe wani mai suna Abba dan shekara 27 da haihuwa ɗan asalin ƙaramar hukumar Funtua.
Haka kuma DSP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa a dai garin na Sabuwa,bayan samun bayanan sirri mamaye ƙauyen Zagaigaza da ‘yan bindiga sukayi,”Yan sandan sun shiga ƙauyen inda bayan musayar wuta,sun sami nasarar kuɓutar da mutane 14 da shanu biyu,”Inji DSP Sadiq.
Amma ya sanar da cewa ‘yan bindigan sun kashe mutane biyu a lokacin musayar wutar.
Kwamishinan ‘yan sanda a jihar CP Bello Shehu ya jinjina wa jami’an sa bisa jarumtaka da namijin ƙoƙarin da suka nuna wajan ceto mutanen.
Ya kuma nemi goyon bayan al’ummar jihar bisa ƙoƙarin da jami’an tsaro keyi na maido da zaman lafiya a jihar.
