Tinubu zai ƙara inganta Arewa da ayyukan raya ƙasa, inji Ministan Labarai

Spread the love

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Shugaba Bola Tinubu zai ƙaddamar da ƙarin ayyuka a yankin Arewa ta hanyar manufofi na gari da shirye-shiryen da suka dace da buƙatun al’umma.

Ministan ya bayyana hakan ne a yayin wata hira a gefen taron kwanaki biyu da aka gudanar a Kaduna, mai taken “Nazarin Alƙawuran Zaɓe: Haɓaka Hulɗa Tsakanin Gwamnati da Jama’a Don Haɗin Kan Ƙasa”, wanda Gidauniyar Sir Ahmadu Bello Memorial ta shirya.

Ministan ya tunatar da cewa tun kafin zaɓen Tinubu, ya ziyarci Kaduna inda ya gana da shugabannin Arewa tare da yin alƙawaran da suka shafi tsaro, noma da tattalin arziƙi.

Ya ce, yanzu gwamnati ta dawo don bayyana irin matakan da aka ɗauka, da abinda za a cigaba da yi.

“Wannan irin haɗakar kai tsaye tsakanin gwamnati da jama’a ba a taɓa yin irin sa ba a baya”, yana mai tabbatar da cewa ba zai tsaya a iya wannan ba.

Ya bayyana cewa, ministoci da dama daga yankin Arewa, da jagorori sama da 60, sun halarci taron domin yin bayani kai tsaye ga al’umma kan abubuwan da gwamnatin Tinubu ta yi da kuma waɗanda za ta yi nan gaba.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya ruwaito, zaman farko na taron ya mai da hankali kan batun tsaro, yayin da zaman na biyu ya tattauna kan tafiyar da mulki da kuma tattalin arziki.

Tawagar gwamnatin tarayya da ke kula da waɗannan fannoni ta gabatar da bayanai kan nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu tun bayan hawanta mulki.

By Babaji