Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Yayin da albarusan sojojin Isra’ila ke dira a kan al’ummar Gaza a gefe guda kuma yunwa na ragargazar mazauna yankin. Kimanin mata da yara dubu 100 ke fama da mawuyacin yanayi na ƙarancin abinci. Babban jami’in hukumar samar da abinci da duniya Ross Smith ya ce Gaza na gab da aukawa mummunan yanayin ƙarancin abinci ko kai tsaye a ce yunwa. Smith ya ce baa bun da ke tafiya a Gaza don ba batun kasuwanni ko a ce wata hada-hada ga shi an takaita hanyoyin isar da kayan agaji. A nan jami’in ya nuna haƙiƙa abun da a ke bukata shi ne buɗe hanyoyin kan iyaka don shigowar kayan abinci da samun amincewa na jami’an tsaro wajen raba abincin. Al’ummar Gaza na cikin yanayi na rashin tabbas dare da rana don koyaushe wani bom zai iya faɗowa ya hallaka su. Ba batun jinya asibiti ko zama a tantunan gudun hijira, sammakal ko ina sojojin Isra’ila ka iya kai harin su wa imam ta jiragen yaƙi ko motocin yaki ta doron kasa. A iya nuna nadamar kasha waɗanda ba su yi laifin komai ba, Isra’ila kan ce kuskure ko za ta gudanar da bincike. Idan kuskure ne me ke kawo maimaita kuskure a kusan kowane lokaci? In kuma bincike a ke yi ina sakamakon binciken? In an samu wasu masu zarmiya wane hukunci a kan ɗauka a kan su? Akwai fa lokacin da wasu sojojin Isra’ila su ka nuna yaƙin nan na Gaza ya isa hakanan zubar da jinin ya yi yawa. Sakamakon waɗannan sojojin shi ne sallama daga aiki. Ita dai gwamnatin Netanyahu ta shahara wajen ina da yaƙi ko kai hare-hare na kashe duk wanda ya dagawa ƙasar yatsa. Idan a na maganar Falasɗinawa duk neman zaman lafiyar su ai ba za su ci gaba da zama bayi a ƙasar su ta gado ba. Kai a je ma kawai Falasɗinawa sun zauna babu gwagwarmayar Hamas, ba yadda za a yi Isra’ila ba ta riƙa cafke matasa ta na zargin su da cewa su na da niyyar kai hari kan muradun Isra’ila. An sha harbe matasa Falasɗinawa kan wani zargi da bai kai ya kawo ba. Idan an kashe Bafalasɗine tamkar an kasha ɗan ta’adda ne ba wani mataki ko tausayi da za a ji. Gaskiya jinin Falasɗinawa fa ya zama kamar na kiyashi don yawan shekarun da a ka yi a na kisan gilla gare su tun wajen 1948 na nuna ba a ɗauke su da daraja ba ko ma dai a ce dama a na son kwace ƙasar su ne da ƙarfin tuwo. Duk wani labara na Falasɗinawa da za ka gani ya shafi kisa ne na mata da ƙananan yara ko daure wani matashi har ya tsufa a gidan yarin Isra’ila. Kazalika duk wanda ya fito da sunan shi ɗan ƙungiyar Hamas ne to an yanke ma sa hukuncin kisa sai jiran lokacin zartarwa. Me manufar Hamas kuma me ya sa a ka kafa ƙungiyar daga marigayi Ahmad Yasin da a ka kashe kan keken sa na guragu lokacin tafiya sallar asuba? Ko me za mu ce kungiyar ta gwagwarmayar kwato hakkin Falasɗinawa ne da a ka danne ta hanyar hana su ƙasar su inda duk wani batu da ya shafi a ba da dama kamar raba ƙasar biyu Isra’ila ta ɗau cangare daya Falasaɗinawa su ɗau ɗaya ɓangaren na samun watsi daga Isra’ila. Abun da Isra’ila ke so ko dai Falasɗinawa su bar yankin su yi gudun hijira a wasu ƙasashen Larabawa ko kuma su riƙa zama kamar bayi a yankunan da su ke rakuɓe. Gwamnatin Falasɗinawa ta birnin Ramallah ƙarƙashin Mahmoud Abbas na irin wannan zama na nuna takaici da baki kan muzgunawar Isra’ila amma ba daga kara. Sau nawa a na batun kafa ƙasar Falasɗinu mai babban birni a gabashin birnin Kudus amma hakan ya kasa tabbata. Kun ga ko Majalisar ɗinkin Duniya irin wannan yanayi ta ke samun kan ta a ciki sai dai nuna takaici don da zarar an zo ɗaukar mataki mai tsauri, Amurka za ta hau kujerar na ki shikenan magana sai ta shiririce. ƙasashen Larabawa ba su da babban matakin da za su ɗauka don yanayin ƙalubalen siyasar duniya mai buƙatar sara da duba bakin gatari don yanyin akasarin su na mulkin mulukiyya. Hakika da zarar ƙasashen Larabawa masu aiki da tsarin sarauta sun nace lallai sai Falasɗinawa sun samu ‘yanci, ƙasashen yamma ka iya kunno mu su wutar su koma tsarin dimokraɗiyya. Mu tuna kuma abun da ya faru ga marigayi shugaban Masar Muhammad Morsi wanda ya bude mashigar Rafah don samawa Falasdinawa sararawa sai kawai a ka kunno ma sa fitina har a ka kifar da gwamnatin sa a ɗan kankanin lokaci da ma ƙarshe ya rasa ran sa gaba daya. Manyan ƙasashe sun mara baya ga gwamnatin soja ta Alsisi da ta amshi madafun iko ta watsar da ta Morsi wacce ta lashe zabe ta hanyar dimokraɗiyya. Shawara ga Falasɗinawa su kara dagewa ga addu’a don neman taimakon Allah ya yaye mu su wannan fitina da ke ɗaukar rayukan su ba yaro ba babba. Mutuwa dai ba bakuwar aba ba ce a tsakanin Falasɗinawa kuma iyaye ma mata kan rungumi gawar ‘ya’yan su, su yi kuka inda su ɗin ma wani lokacin maƙamin ya dira a kan su. Ina yabawa wasu jakadun Falasɗinawa da ke ƙoƙarin fahimtar da duniya asalin abun da ke faruwa a Gaza ko ma kasar ta Falasɗinawa saɓanin yadda a ke nuna ‘yan ta’adda a ke yaka. Kazalika da ganar da duniya waɗanda a ke kashewa a Falasɗinu ba Musulmi ba ne kaɗai har da mabiya addinin Kirista. A na samun wasu mabiya addinin Kirista da ba sa damuwa da ‘yan uwan su Falasɗinawa inda ido rufe su ke marawa Isra’ila baya. Tamkar ma bai cancanta a samu Bafalasɗine ya zama kirista ba. Isra’ila dai kan kai hari kan kowa ba rowan ta da kowaye matuƙar ya na yankin Falasɗinu ko ya na gwagwarmayar tabbatar da kafa ƙasar Falasɗinawa. Amfani da jiragen yaƙi wajen kai hari ga waɗanda ke yawo ko ke yaƙin sari ka noƙe a yankin su na nuna amfani da ƙarfi marar kima da kan kare kan mata da ƙananan yara.
Fafaroma ya buƙaci kawo ƙarshen yaƙin Gaza:
Fafaroma Leo ya buƙaci Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da ya kawo ƙarshen yaƙin Gaza da ke kawo matsala ga rayuwar mazauna yankin.
A wayar tarho, Fafaroma ya yi magana da Netanyahu ne bayan harin da sojojin Isra’ila su ka kai kan majami’ar katolika ita ɗaya tilo a Gaza inda su ka kashe mutum 3.
Fadar ɓatican ta ce Netanyahu ne ya buƙaci zantawar ta tarho don nuna juyayin harin kan majami’ar.
A nan Fafaroma ya buƙaci kula da wajajen ibada a irin wannan yanayi da kuma kare rayukan al’umma.
An ruwaito Netanyahu na nuna nadamar harin da ɗora alhakin haka kan batan kai na albarusai.
Akwai shirin Fafaroma Leo da Netanyahu za su gana kan lamarin na Gaza.
PDP ta Osun ta mara baya ga tazarcen Tinubu a 2027:
Jam’iyyar PDP reshen jihar Osun ta amince da mara baya ga neman tazarcen shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu a babban zaben da ke tafe a 2027.
PDP ce ke da gwamnati a jihar ta Osun da ke kudu maso yammacin Nijeriya ƙarƙashin gomna Ademola Adeleke.
A zaɓen 2023, dan takarar PDP Atiku Abubakar ne ya yi nasara da tazara marar yawa kan shugaba Tinubu na APC.
Kakakin gwamna Adeleke, Adewale Rasheed ne ya karanta matsayar jam’iyyar da nuna duk da haka Adeleke na jam’iyyar PDP don raderadin zai sauya sheƙa zuwa APC ba daga gare ba ne.
Matsayar ta ƙara da cewa Adeleke zai sake takarar gomna a watan Agustar badi a inuwar PDP.
Masu sharhi na ganin hakan a matsayin wasu dabarun siyasa duk da sanarwar na nuna ai jihar Osun gidan shugaba Tinubu ne.
Sanata Natasha ta yi yunƙurin komawa zaman Majalisar Dokoki:
Sanata Natasha Akpoti Uduaghan ta yi yunƙurin komawa zama majalisar dattawa a Talatar nan.
Natasha da rakiyar magoya baya ciki da ‘yar gwagwarmayar siyasa Aisha Yesufu ta yi ƙoƙarin shiga majalisar amma jami’an tsaro ba su ba da dammar hakan ba.
Natasha dai ta na aiki ne da hukuncin babbar kotun tarayya da ta ce umurci dawo da ita majalisar bayan dakatar da ita na tsawon wata 6.
Majalisar dai ta nuna bat a samu umurnin kotun ba kuma matakin Natasha kamar rashin fassara umurnin kotun ne daidai gabanin kammalar wa’adin dakatarwar.
Yunwa ta yi sanadiyyar mutuwar yara 21 a Gaza:
Tsananin yunwa ya yi sanadiyyar mutuwar yara 21 a Zirin Gaza a cikin sa’a 72 kacal kamar yadda majiyoyi daga asibitin Annasr su ka bayyana.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin duniya ke ƙara nuna mawuyacin halin da yaran ke ciki a Gaza.
Kazalika akwai barazanar shigar yunwa don ƙarancin abinci da ke abbadar al’ummar Falasɗinawa a yankin da ke fama da hare-haren Isra’ila.
Alƙaluma sun tabbatar da kasha fiye da mutum 1000 da ke fafutukar karɓar abinci daga wani shirin agaji da Majalisar ɗinkin Funiya ke jagoranta a Gaza.
Sojojin Isra’ila kan kai hari da kan hallaka waɗanda su ka taru a layin karɓar kayan abinci da fakewa da cewa hare-haren na auna ‘yan ƙungiyar Hamas ne.
Jakadiyar tarayyar Turai Kaja Kallas ta yi Allah wadai da kai hare-hare ga waɗanda su ka taru don karɓar kayan agajin abinci.
Kallas ta nuna ba yanda za a kare waɗannan hare-hare don haka ma ta yi magana da ministan wajen Isra’ila Gideon Saar kan buƙatar bada kariya ga masu karɓar kayan agaji ko tabbatar da kare rayukan al’umma a yankin.
Babban Sakataren Majalisar ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da babbar murya na kare mutane masu taruwa don karɓar kayan tallafin.
KAMMALAWA
Saudiyya ta mara baya ga aikin sake gina ƙasar Sham bayan shafe shekaru ta na fama day aikin basasa.
In za a tuna mayakan tahrir sun yi nasarar kifar da tsohuwar gwamnatin Bashar Al’asad inda Ahmad Al-Sharaa ya zama jagoran gwamnatin ƙasar.
A zaman majalisar zartarwar Saudiyya ƙarƙashin jagorancin Sarki Salman, Saudiyya ta ce ya na da muhimmaci a kwantar da duk wata fitina a Sham da taimakawa ƙasar ta sake farfaɗowa kuma tuni Saudiyya ta ware tallafi ga al’ummar Sham.
Kazalika, Saudiyya ta mara baya ga matsayar ministocin wajen kasashe 28 kan kawo ƙarshen yaƙin Gaza da barin kayan agaji su na shiga Zirin.
ƙasar ta Larabawa ta buƙaci ƙasashen duniya su yi tsayin daka wajen ganin lallai Isra’ila ta daina kawo tarnaƙi ga shigar agaji ga al’ummar Gaza.
