Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Haɗin gwiwa na jami’an tsaro da suka haɗa da sojojin sama, ‘yan Sanda, CWC da ‘yan banga sun daƙile yunƙurin kai wasu hare hare a ƙauyen Faskari.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar yan sanda DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar da sanarwar haka,aka kuma rabawa manema labarai a Katsina.
Ya bayyana cewa bayan samun bayanan sirri na yunƙurin kai hari a ƙauyen Unguwar Daudu,”jami’an tsaro ƙarƙashin jagorancin DPO na Faskari suka tunkari ƙauyukan,”inji DSP Sadiq.
“Nan take jami’an tsaron suka sami nasarar fatattakar yan bindiga ba tare da an kashe kowa ba,”ya ce.
A hari na biyu kuwa, DSP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun kai hari a ƙauyukan ‘Yartasha da Buntu a garin Daudawa amma basu sami nasara ba.
Nan ma DPO na Faskari, bayan samun bayanan sirri,cikin gaggawa ya jagoranci sauran jami’an tsaro inda suka sami nasarar fatattakar yan bindigan bayan ɗauka tsawon lokaci ana musayar wuta.
A garin guda biyu da ‘yan bindigan suka kai babu wani jami’in tsaro da ya rasa ransa ko ya sami rauni inji DSP Sadiq.
Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Katsina CP Bello Shehu ya jinjina wa jami’an tsaron bisa ƙwarewa da jarumta da suka nuna wajen yaƙar yan ta’addan.
Ya tabbatar da cewa yan sanda da sauran jami’an tsaro a jihar a shirye suke wajan kare rayuka da dukiyar al’ummar domin haka sai ya nanata kiraye kiraye na neman haɗin kai na al’umma da sauran masu ruwa da tsaki.
