Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Karamar hukumar Safana, a Jihar Katsina tabi sahun ƙananan hukumomin Jibia, Batsari da Ɗanmusa wajen yin sasanci da Fulanin daji masu ɗauke da makamai domin wanzar da zaman lafiya a yankin.
Shugaban ƙaramar hukumar Safana Hon. Abdullahi Sani Safana tare da Yariman Katsina Hakimin Safana Alhaji Sada Rufa’i da Gatarin Katsina Hakimin Zakkah Alhaji Sani Muhammed Zakka suka jagoranci taron tare da Fulanin Daji.
Sun Jagoranci taron a Dajin Gemi tare da Fulanin Dajin a Dajin Gemi dake cikin garin Runka a cikin ƙaramar hukumar ta Safana.
Sun haɗu da juna inda aka tabbatar da yin sulhu tare da yin alƙawarin ɗaukar amanar juna, da amincewa da zaman lafiya a yankin ƙaramar hukumar Safana da kewaye.
A jawabin sa Yariman Katsina Hakimin Safana Alhaji Sada Rufa’i ya gabatar a wajen taron, ya bayyana jin daɗin sa akan wannan sulhu da akayi tare da kira ga Fulanin Dajin da suji tsoron Allah su yadda a zauna lafiya, su kuma yi alƙawarin ba zasu ci amanar su ba.
A nasu ɓangaren, Fulanin Dajin ta bakin shugaba daga cikin ɓangaren su Kachalla Ruga Alhaji Usman ya bayyana cewa” Sun yadda sun amince da sulhu a zauna lafiya, Hausawa manoma kowa yaje gona ya yi hidimar shi hankali kwance, suma a barsu su shiga ko’ina suyi hidimar su hankali kwance.
Sauran Fulanin Dajin da su ka tofa albarkacin bakinsu, a wurin taron, irinsu shugaban matasan Fulanin Dajin Abdulhamid Danda ya ɗauki lokaci mai tsawo yana jawabi, tare da jawo hankalin matasan Fulanin da kuma matasan Hausawa da suji tsoron Allah su bada goyon baya ga wannan sulhu da akayi.
A nashi jawabin, shugaban ƙaramar hukumar Safana Hon. Abdullahi Sani Safana ya bayyana jin daɗin sa akan wannan sulhu da akayi domin wanzuwar zaman lafiya a karamar hukumar Safana, sannan ya yi masu alƙawarin kare mutuncinsu a kowane ɓangaren.
Ya bada umurnin ga ɓangaren ilmi da ɓangaren lafiya na karamar hukumar da suje su binciko halin da makarantun da asibitocin Fulanin Dajin suke ciki domin a gyara su.
Shugaban ƙaramar hukumar ya sanar masu da cewa yanzu za su iya zuwa asibiti su kai iyalansu, da su kansu, za su iya zuwa kasuwa su kai dabbobinsu, da sauran hidimominsu na rayuwa ba tare da wata tsangwama ba, kuma za a gyara masu Dam,domin amfanin su da dabbobin su.
Ƙa’idoji guda ashirin ne kowane ɓangaren zai kiyaye, ɓangaren Fulanin Daji bayan wannan sulhu ba za su ƙara kai hari ko’ina ba, ba za su kara hana manoma noma ba.
Haka zalika ɓangaren mutanen gari Hausawa, ba za su ƙara tsangwamar Fulanin Daji ba, idan sun shigo cikin gari, kamar kowane ɗan ƙasa za su riƙa zuwa kasuwa da su da iyalan su.
Karamar Hukumar Safana na ɗaya daga cikin Ƙananan hukumomin da su ke fama da hare haren yan bindiga da yayi sanadiyar rasa rayuka da dukiya masu ɗinbin yawa.
