Shugaban NULGE a Katsina ya taya shugaban ƙwadago na jihar murnar sarautar Sarkin Gabas

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi a Jihar Katsina kwamred Nasiru Wada Mai’adua ya taya shugaban ƙwadago a jihar kwamred Hussaini Hamisu Yanduna murna bisa samun sarautar Sarkin Gabas na Daura.

Sarkin Daura Farouk Umar Farouk ya tabbatar wa shugaban ƙwadago da sarautar Sarkin Gabas ɗin Daura, kamar yadda Sarkin ya ce a Hussaini Yanduna wannan sarauta ne bisa cancanta da taimakawa masarautar da al’ummar ƙasar Daura da jiha baki ɗaya.

Shugaban, kwamred Nasiru Mai’adua ya bayyana shugaban ƙwadagon a matsayin mutum mai jajircewa wajen nema wa ma’aikata haƙƙin su.

Wannan bayanin ya na ƙunshe ne a wata takardar sanarwa ɗauke da sa hannun shugaban NULGE kuma aka raba wa manema labarai a Katsina.

“Shugaban NLC mutum ne mai gaskiya da riƙon amana kuma baya kyamar kowa,kowa na sa ne,”inji kwamred Wada Mai’adua.

Ya ce haƙurin sa da taimakon al’umma ya sa har masarautar Daura ta karramashi da wannan sarauta.

Kwamred Nasiru Mai’adua sai yayi kira ga sauran masarautu da suyi koyi da masarautar Daura wajen bada sarauta ga masu irin wannan hali na kwamred Hussaini Hamisu Yanduna.

Haka kuma shugaban NULGE a Katsina yayi kira ga al’ummar yankin Daura da na jihar baki ɗaya musamman ya’yan ƙungiyar da su fita kitsan su da kwarkwata ranar bikin naɗi domin su nuna masa karamci da ƙauna.

By ukarofi