Kaduna: ‘Yan sanda sun daƙile shirin sayen ƙuri’u da ƙwato tsabar miliyan N25

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jami’an ƴan sanda a Jihar Kaduna sun yi nasarar kama wani mutum da ke ɗauke da tsabar kuɗi kusan Naira miliyan 26, wanda aka yi zargin da su za a saye ƙuri’u a zaɓen cike gurbi na yau Asabar.

An kama wanda ake zargin, mai suna Shehu Patangi ne a safiyar yau Asabar a wani sanannen Otal da ke hanyar Turunku a garin Kaduna, inda yake shirin raba kuɗaɗen don janye ra’ayoyin masu kaɗa ƙuri’a a Mazaɓar Tarayya ta Chikun/Kajuru.

Kakakin ƴan sandan, DSP Mansir Hassan ya tabbatar da kamen a wata sanarwa inda ya ce, N25,963,000 suka ƙwace a hannun wanda ake zargin.

Patangi a yayin bincike akansa, ya ce ana shirin saye masu zaɓe ne da kuɗaɗen, sannan ya kuma ya nemi a yi masa afuwa.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, Rabi’u Muhammad ya yaba wa jami’an bisa hoɓɓasa da suka yi tsakaninsu da wasu hukumomi wajen cimma nasarar kama mai laifin.

Ya kuma yi gargaɗin cewa hukumar ba za ta lamunci kowane irin yunƙuri na saɓa wa dokokin zaɓe ba, yana mai cewa duk wanda aka kama da ƙarya su zai fuskanci hukuncin doka.

Haka kuma, ya tabbatar wa al’umma cewa sun ɗauki matakan da suka dace wajen bai wa rayuka da dukiyoyinsu tsaro yayin gudanar da zaɓen tare da kira a gare su da su fito ƙwansu da ƙwarƙwata wajen zaɓar waɗanda suke so.

By Babaji