Daga UMAR GARBA a Katsina
Gwamnatin Katsina ta bayyana cewa mutane 62 da aka yi garkuwa da su sun kuɓuta daga wurin da ‘yan bindiga ke tsare da su bayan wani hari ta sama da sojoji suka kai a sansanin wani ƙasurgumin ɗan bindiga, Muhammadu Fulani, a ƙaramar hukumar Ɗanmusa ta jihar.
Dr Nasir Mu’azu, kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar yau Litinin a Katsina.
Sojojin saman Najeriya sun kai farmakin ne a yankin Jigawa-Sawai da ke kan iyaka da Jihar Zamfara.
Kwamishinan ya ce mutane 12 daga cikin waɗanda suka tsere a halin yanzu suna samun kulawar likitoci a babban asibitin Matazu, yayin da wasu 16 kuma suna sansanin rundunar sojojin Najeriya na Forward Operational Base (FOB) da ke kai ga Malamai.
“Harin rundunar sojojin saman Najeriya da aka ƙaddamar a ranar Asabar da misalin ƙarfe 05:10 na yamma, ya tilastawa ‘yan bindigar tserewa daga maɓoyarsu, lamarin da ya ba wa mutanen da ake garkuwa da su damar tserewa.
“A hirar da aka yi da waɗanda aka ceto, sun tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun gudu ne sakamakon harin da jirgin yaƙin ya kai.
“Waɗanda lamarin ya rutsa da su sun bayyana cewa mutane kusan 62 ne suka tsere kuma suka bi ta hanyoyi daban-daban don tsira daga sansanin ‘yan bindigar.
“Mafi yawan waɗanda ake garkuwar da su sun ce an sace su ne daga ƙauyen Sayaya yayin wani hari da daddare da aka kai musu a ranar Litinin, 11 ga watan Agusta, 2025, da ‘yan bindigar su ka kai Matazu, da Kankia, da Dutsinma, da kuma wasu sassan Jihar Kano,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta tura da rundunar ‘Quick Response Wing’ na rundunar sojojin saman Najeriya domin dawo da zaman lafiya a cikin al’ummomin da ke fama da rikici a ƙananan hukumomin Bakori da Matazu.
“A halin yanzu sojojinmu suna sanya ido kan lamarin don ci gaba da ayyukan ceto,” in ji shi.
