
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ooni na Masarautar Ife, wato Oba Adeyeye Ogunwusi ya yi wa Alafin na Oyo, Oba Abimbola Owoade martani bisa kalamansa na umarnin ya soke sarautar Okanlomo na ƙasar yarbawa da ya bai wa ɗan kasuwa Dotun Sanusi da ake kira da Ilaji.
A ranar 18 ga watan Agusta, 2025 Alafin na Oyon ya nemi Oonin da ya gaggauta soke bada muƙamin, inda gargaɗe da cewa ya yi hakan cikin kwana biyu ko kuma ya fuskanci hukunci.
Da yake magana a ranar Talata, Oonin ya bayyana hakan a matsayin abinda ba shi da tasiri ga hukuncin nasa.
Sarkin, ta kakakinsa, Otunba Moses Olafare a wani rubutu a Facebook, ya bayyana Oba Owoade a matsayin ɗan barƙwanci.
Olafare ya ce, mai gidan nasa ya umarce shi da kada ya yi magana akan abinda ya kira da barazanar da ba ta da tasiri akansa.
Ya ce, Oba Owoade kamar Alawada Babasala yake, wato wani marigayin ɗan barƙwanci na yarbawa da aka yi a wani lokaci da ya shuɗe.
