Zaɓen Zamfara: Ba na’urar BVAS ba zaɓe, inji APC

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jam’iyyar APC reshen Zamfara ta yi watsi da matakin da gwamnatin jihar ta ɗauka na tursasa wa hukumar zaɓe ta ƙasa INEC cewar ta gudanar da zaɓen cike gurbin ɗan majalisar jihar shiyyar Ƙaura Namoda ta Kudu da za a gudanar ranar Alhamis ba tare da amfani da na’ura mai tsarin tantance masu kada ƙuri’a na BVAS ba.

Jam’iyyar ta ce, babu BVAS babu zaɓe, lura da cewa a zaɓen da aka yi a ranar 16 ga watan Agusta da ya gabata an samu kura-kurai daga dukkan jam’iyyu amma babu wanda ya koka game da amfani da BVAS.

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar na jihar Yusuf Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Gusau yau Laraba.

“Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta samu sahihan bayanai daga fadar gwamnatin jihar kan wani taron da aka gudanar a daren jiya zuwa misalin ƙarfe 3 na safiyar Talata (19/8/2025) tsakanin kwamishinan zaɓen INEC da gwamnatin jihar da kuma jam’iyyar PDP a ɗaya ɓangaren.” Yace

” Kuma mun gano Wani yunƙurin almundahana da gwamnatin jihar suke shiryawa na ganin sun tursasawa hukumar zaɓe cewar kar tayi amfani da na’urar BVAS wajen tantance masu kaɗa ƙuri’a lokacin da za a kammala zaɓen cike gurbin a ranar Alhamis.”

Jam’iyyar ta kuma ƙalubalanci shirin gwamnatin jihar na cewa jami’an tsaron gidan gwamnati ne kawai za a yi amfani da su, musamman ‘yan sanda da DSS a lokacin zaɓen.

“Mun riga mun bayar da rahoton yunƙurin da gwamnatin jihar ta ke son yi na shigar CSO da ADC na gwamna wajen jagorantar wasu jami’an tsaro da ’yan daba don hargitsa zaɓukan da za a sake kammalawa ranar Alhamis kasancewa a jam’iyyar APC ita ke da ƙuri’u mafi rinjaye a zaɓen da ya gabata”. Cewar Yusuf

Jam’iyyar ta yi kira ga shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) da ya dakatar da shugaban hukumar zaɓe ta Zamfara daga cikin zaɓen da za a sake yi, sannan ya aiko da wani mutum da zai gudanar da zaɓen ta hanyar amfani da BVAS wanda ko APC ko PDP ba ta taɓa shakkar hakan ba a zaɓen da ya gabata 16 ga Agusta.

Da ya ke zantawa da manema labarai a kan lamarin, kwamishinan zaɓe na Zamfara, Dakta Mahmud Isah, ya musanta yin wata ganawa da gwamnatin jihar kamar yadda APC ta yi zargin.

By ukarofi