‘Yan bindiga sun ƙona mutane 20 da ransu, bayan kashe masallata 30 a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Mazauna ƙaramar hukumar Malumfashi da ke Jihar katsina na ci gaba da kokawa kan yadda ‘yan bindiga suka addabi ƙauyukan yankin da kai hare-hare.

Ɗan majalisar da ke wakiltar ƙaramar hukumar Malumfashi a majalisar dokokin jiha, Hon. Aminu Ibrahim, ya bayyana cewa an tafka ɓarna a cikin hare-haren da aka kai na baya-bayan nan, ya bayyana cewa a wani harin da ‘yan bindigan suka kai, sun cinna wa mutane wuta da ransu saboda rashin imani.

Hon. Aminu Ibrahim ya bayyana cewa adadin mutanen da ‘yan bindigar suka kashe a hare-haren da suka kai a mazaɓar sa ya ƙaru zuwa mutum 50.

A cikin wani bidiyo da shafin Facebook na ‘Katsina State House of Assembly Media Centre’ ya wallafa, an nuna ɗan majalisar ya na jawabi ga takwarorinsa a zauren majalisar.

Mutanen an kashe su ne a hare-hare daban-daban da ’yan bindiga suka kai a ƙaramar hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina.

Hon. Aminu Ibrahim ya ce ’yan bindigan da ke ɗauke da makamai sun kashe masallata 30, sannan suka ƙone wasu mutum 20 da ransu.

Ɗan majalisar ya ce hare-haren da aka kai a gidan Adamu Mantau, Unguwar Yar Mai Dabo, da ƙauyen Makera a gundumar Karfi, da kuma ƙauyen Burdigau a gundumar Yaba, sun bar jama’a cikin tsananin fargaba da baƙin ciki.

Cewar Aminu Ibrahim, mazauna ƙauyukan sun sanar da ganin giftawar ’yan bindiga a kusa da Burdigau tsakanin ƙarfe 6:00 zuwa 7:00 na yamma a ranar Litinin, amma sai daga baya sojoji suka iso, sannan suka janye ba tare da tabbatar da tsaro ba a yankin ba.

A cewarsa, da safiyar ranar Talata, ’yan bindigan suka kai farmaki a Unguwar Mantau, inda suka bindige masallata 30 a yayin sallar Asuba.

“Lamarin ya kai maƙura, mutanenmu ba za su iya ci gaba da zama a ƙauyukansu ba saboda waɗannan hare-haren marasa ƙarewa.” In ji shi.

Ɗan majalisar ya roƙi gwamnati da ta kafa sansanin tsaro na dindindin a gundumomin Karfi da Yaba domin shawo kan matsalar.

Bayanin nasa dai ya tayar da hankalin ’yan majalisa kan yadda jinin al’ummar Katsina ke ta zuba duk da ayyukan sojoji da ake ci gaba da yi.

By ukarofi