Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Idan mutum mai son zuciya ya samu rana sai ya shanya sharrin sa da tunanin zai iya cin duniyar sa da tsinke ba tare da samun katsalandan ɗin hatta wadanda ya ke takewa hakki ba. A zahiri wannan shi ne abun da Isra’ila ke yi a cikin Sham da kuma nan Gaza.
Yanzu don Isra’ila ta kai hari tsakiyar Damaskas ko kan Falasɗinawa a Gaza ba ma wani babban labara ba ne don ya zama rowan dare game duniya.
Koma su waye sojojin Isra’ila su ka kashe a Sham ko Gaza ba bin kadu don Isra’ila za ta ce ta na farautar sauran mayakan Iran ne a Sham ko neman magance mayaƙan Hamas a Gaza. Isra’ila kan samu mara baya na Amurka ko da an kai wani ƙuduri na neman taka ma ra birki a kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin Duniya.
Ba ma wani bambancin takun Amurka zamanin tsohon shugaba Joe Biden na Dimokrats da shugaban da ke gado Donald Trump na Rifabulikans. Mara baya ga Isra’ila na cikin manufofin gwamnatin Amurka. Kuma dakile yunkurin samun maslahar kafa ƙasar Falasɗinu ya zama manufa a Amurka. Manyan ƙasashen Larabawa na da burin ganin an kafa ƙasar Falasɗinu mai cikekken ‘yanci gefe da Isra’ila don a huta da ce-ce-ku-ce kan halin da Falasɗinawa ke ciki.
Tabbas in an kafa ƙasar Falasɗinu, Larabawa za su samu damar taɓukawa ta tallafa wa tattalin arzikin Falasɗinawa ba tare da batun yaƙi ba. Wato sai ya zama ba hannun Isra’ila a lamarin kowa ya yi harƙar sa. A yanda lamura su ke tafiya a yanzu zai yi wa Larabawa wuya su iya fito na fito da Isra’ila in ka deɓe bayanai irin na diflomasiyya. Idan za a yi wa ƙasashen adalci an san ba zai yiwu su iya ƙasadar samun sabani da Amurka ba don yin hakan ka iya jawo barazana ga wanzuwar gwamnatocin su musamman na mulkin mulukiyya.
A zamanin yau tamkar mulkin mulukiyya na neman zama tsohon ya yi don haka duk ƙasar da ke irin wannan mulkin sai ta zama mai cizawa da hurawa. Wasu gwamnatocin kuma na Larabawa da ba mulukiyya ba kamar Masar na samun ɗaurin gindin Amurka ne don biyan muradun kare Isra’ila daga duk wani daga yatsa daga wadanda ke ganin an zalunci Falasɗinawa.
Mu tuna abun da ya faru ga zaɓaɓciyar gwamnatin dimokraɗiyya ta Muhammad Morsi a Masar wacce duk da ta bi tsarin yammacin duniya wajen lashe zabe amma ta kasa iya mulkin ƙasar don tsoma baki daga ƙetare inda a ka amince sojoji su ka kifar da gwamnatin da samun mara baya nan take daga manyan na ƙetare.
Ashe ba lallai lashe zaɓe ne kan wanzar da gwamnati ba akwai kare muradun gagararrun ƙasashe na ketare masu ƙarfin faɗa a ji ko ba a so a duniya. Don haka in an zo sharhi kan ƙasashen Larabawa a rika la’akari da asasin gwamnatocin da kaucewa tsananta tunani ko ma la’antar ƙasashen da ganin ko sun watsar da ‘yan uwan su Falasɗinawa. Ko Turkiyya da ke taɓukawa don ba ƙasar Larabawa ba ce turawa ne kuma ba mulkin mulukiyya ta ke yi ba.
ƙasar Turkiyya da Siriya sun gargaɗi Isra’ila da ta daina kai hare-haren neman ƙara cinna wuta a Siriya da tuni yaƙi ya daidaita. Ministan wajen Siriya wato Sham da takwaran san a Turkiyya ne su ka yi gargaɗin a taron manema labaru a birnin Ankara na Turkiyya.
Ministan wajen Turkiyya Hakan Fidan ya aza alhakin neman birkita Sham kan ƙasar Isra’ila da nuna ba za a lamunci hakan ba. Kazalika Fidan ya kara jaddada matsayar ƙasar sa cewa ba za ta amince da turjiyar mayaƙan Kudawa na PKK da ke hada-hadar su a yankin arewa maso gabashin Sham ɗin ba.
Fidan ya ce tamkar birkita ƙasar Siriya na daga abun da Isra’ila ke maida fifiko a kai da ɗaukar hakan na da amfani ga tsaron Isra’ilar. A cewar Fidan tun kawar da gwamnatin Bashar Al’Asad, Isra’ila c eta zama babbar mai kutse wajen hargitsa lamura a Sham.
Ministan wajen Sham Asaad Al-Shaibani ya ce Sham na fuskantar tsoma baki na kai tsaye da a kaikaice daga ketare da zummar kunna Karin fitina a ƙasar.
Al-Shaibani ya yi magana kan yankin masu bin addinin DRUZE da ke kudu maso yammacin Sham da nuna lallai hakkin Sham ne kawo salama a yankin don mallakar ƙasar Sham ɗin ne.
Al-Shaibani ya ƙara da nuna shirin ladabtar da waɗanda su ka haddasa fitina a yankin na Druze na mabiya wata ɗarikar da ta samo asali daga Ibraniyanci masu imanin in an mutu a kan iya dawowa rayuwa a duniya.
Turkiyya na kan gaba a ƙasashen da su ka ba da gudunmwa wajen kawar da gwamnatin Damaskas ta Al’Asad inda jagoran mayaƙan Tahrir wato Ahmad Al-Sharaa ya zama muƙaddashin shugaban ƙasar.
Yayin da Al-Sharaa ya samu ganawa da Donald Trump a birnin Riyadh, shi kuma tsohon shugaban Sham Bashar Al’Asad na samun mafakar siyasa a wajen shugaba Putin a Masko.
Majalisar Zartarwar lamuran tsaro ta Isra’ila ta yanke matsayar amshe iko da Garin Gaza wanda shi ne ya fi yawan jama’a a Zirin Gaza.
Wannan na daga matakan ci gaba da yaƙin wata 22 da ya faro tun daga kutsawar Hamas cikin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktobar 2023.
Bisa alkaluman ma’aikatar lafiya ta Gaza, yakin dai zuwa yanzu ya yi sanadiyyar kashe fiye da Falasɗinawa 61,000 da jefa Zirin cikin yunwa don tsananin karancin abinci inda mutane kan kanjame su mutu don rashin samun abinci na kwanaki.
Gabanin fara taron majalisar tsaron a alhamis ɗin makon jiya, Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce gwamnatin sa na son mamaye dukkan Gaza ta hanyar kwace Zirin inda za ta mika ragamar sa ga wasu dakarun Larabawa da ba sa ga-maciji da Hamas “mu na son karɓe Gaza don tabbatar da tsaron mu, mu kawar da Hamas daga Zirin, mu ba wa al’umma aminci daga Gaza” inji Netanyahu “mu na son miƙa Gaza ga sojojin Larabawa da za su mulki yankin yanda ya kamata ba tare da yi ma na bazaraba ba; inda za su samawa Gazawa rayuwa mai kyau”
Wani Janar na sojan Isra’ila ya nuna fargabar karɓe ikon Birnin Gaza ko daukacin Zirin zai jefa rayuwar kimanin kamammun Isra’ilawa 20 da ke hannun Hamas cikin hatsari, hakanan zai kara wahalar da sojojin kasar da ke yaƙi na tsawon watanni.
‘Yan uwan kamammun ma na adawa da wannan shirin na Netanyahu wanda har ya jawo zanga-zanga a gewayen ɗakin da a ke gudanar da taron na tsaro.
Ba a san adadin mutanen da ke zaune a Gaza-Gari ba tun da an sha umurtar jama’a su fice daga garin amma wasu sun dawo a lokacin da a ka samu tsagaita wuta da shirin ya wargaje inda Isra’ila ta cigaba da rowan boma-bomai kan sassan Gaza “ba sauran wajen da ba a mamye ba a Gaza, ai ba ma abun da ya saura na Gaza” inji Maysaa Al-Heila da ke zaune a sansanin gudun hijira.
Yankunan Gaza sun hada da Gaza-Gari, Jabalia, Khan Younis, Rafa, Deir al-Balah da Bait Hanoun.
Sojojin Isra’ila kan buɗe wuta kan masu taruwa don gwagwarmayar samun tallafin abinci inda ta kashe fiye da Falasdinawa 1000.
Batun taron tsagaita wuta a birnin Doha da Masar da Katar ke jagoranta tare da sa hannun Amurka ya shiga tangal-tangal don rashin samun cimma sharadin Isra’ila na lallai Hamas ta wargaza mayakan ta.
Hamas dai ta ce ba za ta daina gwagwarmaya ba sai an kafa kasar Falasɗinu mai babban birni a gabashin Birnin Kudus.
Jirgin sama daga kasar Jodan ya cigaba da shawagi don jefa tallafin kayan abinci ga al’ummar Gaza daga cikin mawuyacin yanayi na yunwa.
Jirgin kan taso daga Jodan da ke makwabtaka ya bi samaniyar Gaza ya na jefa kayan tallafi a sassan da sun zama kangaye.
Dakatar da shigar da tallafi yankin na tsawon wata 9 da Isra’ila ta yi ya jawo yunwa ta addabi al’umma kuma hakan salon Isra’ila ne da zummar murkushe Hamas.
Jodan na haɗa kai da wasu kasashe wajen aikin jefa kayan agajin kuma a baya ma Sarki Abdullah da kan sa ya shiga jirgi don jefa kayan agajin.
Rundunar tsaron lafiyar farar hula a Gaza ta baiyana cewa wani harin da Isra’ila ta kai Zirin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 34.
Kakakin rundunar Mahmud Bassal ya ce cikin wadanda harin ya kashe akwai mutum 9 da ke jiran karɓar kayan agajin abinci a mashigar arewacin Gaza ta Zikim inda kuma harin ya raunata wasu mutum 181.
Fiye da mutum 12 da a ka kashe farar hula ne sannan wani harin a tsakiyar Gaza ya yi sanadiyyar kisa ga Falasɗinawa 6 da raunata wasu mutum 30.
Kullum dubban mutane kan taru a wajen karɓar kayan agaji inda 4 daga cikin su Amurka da Isra’ila ke kula da su.
Rundunar sojan Isra’ila kan ce ta na harbi ne don hana cunkoso amma hakan ya yi sanadiyyar kashe fiye da mutum 1000.
KAMMALAWA
Sabon harin da sojojin Isra’ila su ka kai kan Gaza ya yi sanadiyyar kisan gilla ga Falasɗinawa 123 a Gaza.
Wannan dai ya zo ne gabanin shirin karɓe Gaza da Isra’ila ke shirin yi don muradin murƙushe duk wata gwagwarmaya ta Hamas.
Wannan kisa cikin sa’a 24 shi ne mafi muni a lokaci daya tun sabon yaƙin da ya barke kimanin shekaru 2 da su ka wuce da ya kawo tsanantar rayuwa ga mazauna Gaza miliyan 2.
A yayin da wannan ke faruwa, wakilan Hamas na ganawa da masu shiga tsakani na Masar don samun tsagaita wuta.
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu na ƙarfafa manufar da shugaban Amurka Donald Trump ya kawo na al’ummar Gaza su fice daga Zirin salun-alun.
Netanyahu ya ce duk ƙasashe masu maraba da karɓar Falasɗinawa su buɗe ƙofar su kawai don karɓar Falasɗinawan su kuma daina yi wa Isra’ila surutai.
ƙasashen Larabawa da wasu da dama a shugabannin duniya na ƙin jinin duk wani shiri na kaurar da Falasɗinawa daga ƙasar su ta gado.
Hatta gwamnatin Falasɗinawa ta Mahmud Abbas a birnin Ramallah na ɗaukar kawar da Falasɗinawa a Gaza tamkar yakin da ya auku ne 1948 inda a ka tilastawa dubban Falasɗinawa barin ƙasar su a arangamar da a ke yi wa taken NAKBA.
Majiya na nuna kwace Gaza zai faru a ‘yan makwanni in ba dai an samu cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ba, da ke samun cikas don sharaɗin Isra’ila na neman wargaza Hamas; inda ita kuma Hamas ta ce faufau hakan ba mai yiwuwa ba ne.
