An yi kira ga gwamnatin Katsina ta gina hanyar zamani daga Gurbin Ɓaure zuwa Batsari

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Jibiya Mustapha Yusuf Jibiya da takwaransa na ƙaramar hukumar Batsari Hon. Mustapha Tukur Ruma su ka gabatar da ƙudirin neman gina hanyar.

Ɗan majalisar Jibiya ya bayyana cewa an bada kwangilar gina wannan hanya a gwamnatin da ta gabata amma matsalolin rashin tsaro da su ka addabi yankin, aikin hanyar ya sami tsaiko.

“Amma kasancewar samun tsaro a yankin yasa muka sake gabatar da ƙudirin na buƙatar gina hanyar a halin yanzu,”inji ɗan majalisar.

Aikin hanyar in ya sami amincewar gwamnati, zai tashi daga Gurbin Ɓaure zuwa garuruwan Shimfiɗa,Farfara,Garin zaki,Garin Labo zuwa Batsari.

Haka kuma yan majalisar ƙananan hukumomin Dutsi Mani sun gabatar da ƙudirin buƙatar gwamnatin jihar da ta gina hanyar da ta tashi daga Dutsi, Ɗan Kemu, Randawa, Walawa, Asingiri, Magami zuwa Mani, dukkansu dake cikin ƙaramar hukumar Dutsi da Mani.

Duk a zaman majalisar ,ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Ɓatagarawa Hon. Tukur Ilyasu Shagumba ya gabatar da ƙudirin buƙatar kai agajin gaugawa ga al’ummar Makada dake cikin mazaɓar Dabaibayawa a ƙaramar hukumar Ɓatagarawa.

Shi ma ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Malumfashi Hon. Aminu Ibrahim Malumfashi ya gabatar da ƙudirin buƙatar gina hanya da tashi daga Na Awaki, Gundurawa, Dokoki, Lamuntani, Kuba Hazo, Gidan Liti, zuwa Gangara, duka a cikin mazaɓar Gora dake cikin ƙaramar hukumar Malumfashi.

Bayan da majalisar ta tattauna akan ƙudurorin,ta amince dasu, inda Kakakin majalisar ya umurci akawun majalisar da ya tura ma ɓangaren zartarwa domin ɗaukar matakin da ya dace.

By ukarofi