Gwamna Raɗɗa ya amince da naɗin manyan mataimaka na musamman guda 15

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

A wata sanarwa ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labarai na gwamnan Muhammad kaula ya bayyana cewa Hon Mannir Shehu Wurma shine babban mataimakin na musamman kan yaɗa labarai.

Sauran waɗanda kusan dukkan su tsaffin shugabannin ƙananan hukumomi ne,akwai Hon Bala Garba Tsanani a matsayin mataimaki na musamman kan harkokin jami’ya.

Sai Aminu Ashiru Mani harkokin SPIME da Rabi’u Aliyu Kusada mataimaki na musamman kan hukumar otel na gwamnati.

Akwai Hajiya A’isha Barda mataimakiya ta musamman kan shirin ciyar da ɗalibai.

Sauran kuwa sun sami muƙaman mataimaka na musamman kan shirin cigaban al’umma a ƙananan hukumomin jihar da kowanne su zai riƙe ƙananan hukumomin da suke ƙarƙashin mazaɓar yan majalisar wakilai na ƙasa.

Sun haɗa da Hon Musa Ado Faskari,Hon Nu’uman Imam Muhammad,Hon Dr Habibu Abdulkadir da Hon Ali Mamman Bakori da Hon Labaran Magaji Ingawa.

Sai Bashir Sabi’u Jibiya da Murtala Adamu Ɓaure, Yusuf Mamman Ifo,Sanusi Dangi Abbas da Hon Faruk Hayatu ɓangaren ci gaban matasa.

Gwamna Dikko Raɗɗa ya buƙaci su da su rungumi shirin nan na “gina makomar al’ummar” da sadaukar da kai wajen ciyar da jihar gaba.

By ukarofi